An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 24 March 2016 17:12

Kungiyar Boko Haram ta fitar da Wani sabon faifan bidiyo

Kungiyar Boko Haram ta fitar da Wani sabon faifan bidiyo
Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo da ke tabbatar da cewa shugaban Kungiyar Abubakar Shekau na raye.

A baya dai an saba ganin shugaban kungiyar ta boko haram Abubakar Shekau cikin kuzari a faifan videon da kungiyar ke watsawa , to sai dai a wannan karo sabon bidiyon na kusan minti takwas ya nuna shi a cikin wani yanayi da ke nuna cewa kungiyar ta Boko Haram na cikin wani hali na damuwa.

Shekau wanda ya yi magana da harshen Larabci da Hausa a cikin bidiyon ya ce, Shi ne baban Muhammad, Abubakar dan Muhammad Shekau, jagoran kungiyar nan da ake kira kungiyar Ahlu sunna lil da'awati wal jihad wato masu da'awar yin jihadi . Sannan ya mika gaisuwa ga magoya bayansa tare da tunatar da su da su ji tsoron Allah kuma ya tabbatar musu da cewa yana raye ba kamar yadda aka dinga watsawa a baya ba na cewa ya rasu.

Abubakar Shekau ya jima bai fito a bidiyon kungiyar ba, tun bayan da kungiyar ta yi mubaya'a da kungiyar ISIS a shekarar 2015.

Hotan bidiyon da kungiyar ta watsa ya nuna Abubakar Shekau sanye da kakin soja da kuma rawani a kansa ga kuma bindiga a kafadarsa ta hagu, sannan kuma an jingine tutar Boko Haram a bangarensa na dama.

A baya dai sojojin Najeriya sun sha ikirarin cewa sun hallaka shugaban kungiyar ta boko haram Abubacar Shekau.

Add comment


Security code
Refresh