An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 24 March 2016 14:51

An kame Mutane 9 kan zarkinsu da alaka tare da Kungiyar ISIS a kasar Marocco

An kame Mutane 9 kan zarkinsu da alaka tare da Kungiyar ISIS a kasar Marocco
Gwamnatin Marocco ta sanar da kame mutane 9 kan zarkinsu da alaka tare da kungiyar Ta'addancin nan ta ISIS.

Kamfanin dillancin Labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto ma'aikatar cikin gidan Marocco cikin wani bayyani da ta fitar yau Alkhamis na cewa wadannan mutane 9 da aka kame na shirye-shiryen kai harin ta'addancin a cikin kasar da wasu kasashen waje guda uku.

Har ila yau sanarwar ta tabbatar da cewa 'yan ta'addar na shirin zuwa kasar Libiya domin samun horo na musaman bayan sun kai hare-haren ta'addancin, saidai jami'an leken asirin kasar tare da taimakon Al'umma sun samu nasarar cabke su.

Ma'aikatar cikin gidan ta Marocco ta sanar da cewa daga shekarar 2013 zuwa yanzu sama da kungiyoyin 'yan ta'adda 30 ne suka wargaza tare kuma da dakile wasu hare-haren ta'ddanci da aka yi shirin kaiwa a ciki da wajen kasar.

Add comment


Security code
Refresh