An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 24 March 2016 09:44

Gwamanatin Kasar Ghana Ta Sanar Da Daukan Tsauraran Matakan Tsaro A Kasar

Gwamanatin Kasar Ghana Ta Sanar Da Daukan Tsauraran Matakan Tsaro A Kasar
Gwamnatin kasar Ghana ta gabatar da wani kuduri ga majalisar dokokin kasar don amincewa da shi da nufin kara sanya ido a duk fadin kasar biyo bayan hare-haren ta'addanci na baya-bayan nan da aka kai wasu kasashen da suke yammacin Afirka.

Kafar watsa labaran Africa Times ta bayyana cewar kudurin da gwamnatin kasar Ghana ta mika wa majalisar ya kumshi ba wa jami'an tsaron kasar damar sanya ido da kuma binciken sakonnin da ake aikewa da su ta hanyoyin sadarwa a kasar da suka hada da ta wayar tarho da kuma emails.

Gwamnatin dai ta ce hakan zai taimaka mata wajen magance laifuffuka irin su ta'addanci, satar kudade, fasa kwabrin muggan kwayoyi da dai sauransu.

'Yan adawa a kasar Ghanan dai ciki kuwa har da wasu daga cikin 'yan majalisar sun nuna damuwarsu kan wannan kuduri suna masu cewa hakan yana iya zama leken asirin mutane wanda kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaban majalisar kasar Ghanan dai Edward Doe Adjaho ya ce za su duba lamarin da idon basira don haka kada 'yan kasar su damu.

Add comment


Security code
Refresh