An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 24 March 2016 04:52

Yemen : Bangarorin Da Ke Rikici Sun Amunce Da Tsagaita Wuta

Yemen : Bangarorin Da Ke Rikici Sun Amunce Da Tsagaita Wuta
MDD ta sanar cewa bangarori da ke rikici a kasar Yemen sun amince su tsagaita wuta a ranar 10 ga watan Afrilu mai shirin kamawa.

wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka amunce da ranar 18 watan a matsatin ranar da za' a fara tattaunawar sulhu a kasar Kuwait, domin kawo karshen rikicin da aka shafe shekara guda ana yi.

kamar yadda mai shida tsakani a rikicin kasar ta Yemen na MDD, Ismaïl Ould Cheikh Ahmed ya sanar jiya Laraba a birnin New York ya ce dukkan bangarorin biyu sun amunce da shiga wannan tattaunawar ta gaba- da- gaba da nifin kawo karshen zubar da jini a wannan kasa.

Kazalika babban jami'in yayi fatan wannan matsayar zata bada damar isar da kayan agaji cikin gaggawa ga milyoyin al'ummar kasar ta Yemen da ke cikin sananin bukata tainako.

Alkalumen da MDD ta fitar sun nuna cewa akalla mutane 6000 ne suka rasa rayukansu kana wasu dubbai suka kauracewa muhalen su a yakin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ke yi tun a cikin watan Maris na 2015 da 'yan gwagwarmaya neman sauyi na kabilar Houthi.

Add comment


Security code
Refresh