An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 24 March 2016 03:55

Clinton Ta Cacaki Tsarin Turai Na Yaki Da Ta'adanci

Clinton Ta Cacaki Tsarin Turai Na Yaki Da Ta'adanci
Tsohuwar sakatariyyar gwamnati kana 'yar takarar shugaban kasa a Amurka, Hillary Clinton ta soki tsarin kasashen Turai da jan-kafa wajen yaki ta'adanci.

Mme Cliton wace ke martani kan harin Brussels ta ce dole ne kasashe mambobin kungiyar tarayya Turai sun sake wani sabon tsari na yakar ta'adanci.

Yayinda take bayyana hakan a wani taron yaki da ta'adanci a yankin Californiya Cliton ta ce Amurka na bukatar hadin gwiwa da Turai musamen ta bangaren musayar bayanai domin dakile ayyukan ta'adanci tun daga tushen su.

Kazalika a cewar Cliton akwai bukatar bakunan Turai sun dakatar da samar da kudade ga 'yan ta'ada, sanan kuma a cewar ta ya kamata jiragen yakin Turai sun shiga yakin da ake da 'yan ta'ada a kasashen Iraki da Syria, sanan dakarun na Turai suma su shiga aikin bada horo da taimakawa sojojin dake kasasshen dake yaki da kungiyar 'yan ta'adan (IS).

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh