An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 23 March 2016 16:42

An Samu Hasarar Rayuka A Gumurzu Tsakanin Jami'an Tsaron Somaliya Da 'Yan Al-Shabab

An Samu Hasarar Rayuka A Gumurzu Tsakanin Jami'an Tsaron Somaliya Da 'Yan Al-Shabab
Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron gwamnatin Somaliya da 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab ya lashe rayukan 'yan ta'adda da dama gami da na jami'an tsaron kasar.

Shafin watsa labaran Al-Yaumus-Sabi'i na kasar Masar ya bada labarin cewa; Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron gwamnatin Somaliya da 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab ta kasar a kauyukan da suke arewa maso gabashin kasar ta Somaliya ya lashe rayukan 'yan ta'adda akalla goma tare da samun nasarar kame wasu fiye da 100 na daban.

Shaidun ganin ido sun bayyana cewa; Gumurzun ya lashe rayukan jami'an tsaron kasar ta Somaliya amma babu hakikanin adadinsu. A cikin 'yan watannin baya-bayan nan jami'an tsaron Somaliya da taimakon dakarun kungiyar tarayyar Afrika sun tsananta kai hare-hare kan yankunan da 'yan ta'addan Al-Shabab suka mamaye a kasar.

Add comment


Security code
Refresh