An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 23 March 2016 16:28

Gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya Tana Ci Gaba Da Rusa Gidajen Palasdinawa

Gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya Tana Ci Gaba Da Rusa Gidajen Palasdinawa
Majiyar Hukumar Palasdinawa ta sanar da cewa: Manyan motocin rusa gine-gine wato bulldozer sun shiga kauyen Da'na da ke gabar yammacin kogin Jordan, inda suka rusa gidajen Palasdinawa masu yawa.

Babban jami'in Hukumar Cin Kwarya-Kwaryar Gashin Kan Palasdinawa da ke kula da bangaren yankunan Palasdinawa da aka mamaye a gabar yammacin kogin Jordan Ghassan Daghlis a yau Laraba ya bayyana cewa; A cikin watan da ya gabata mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun tura manyan motocin bulldozer har sau uku suna zuwa kauyen Da'na da ke gabashin garin Nablus a gabar yammacin kogin Jordan, inda suke rusa gidajen Palasdinawa.

Ghassan Daghlis ya kara da cewa: Mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna rusa gidajen Palasdinawan ne bisa da'awar cewa an gudanar da gine-ginen ba a kan ka'ida ba, lamarin da ya janyo daruruwan mutane da suka hada da mata da tsofaffi gami da kananan yara suka rasa makwanci a kauyen.

Add comment


Security code
Refresh