An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 23 March 2016 15:33

Jiragen Saman Yakin Masarautar Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kasar Yamen

Jiragen Saman Yakin Masarautar Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kasar Yamen
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen.

Shafin watsa labaran Saba na kasar Yamen ya watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya da kawayenta sun kai jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankunan garin Ta'az da ke kudancin kasar Yamen a yau Laraba, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu adadi masu yawa baya ga rushe-rushen gidajen jama'a, cibiyoyi da hanyoyin zirga-zirga.

Manufar tsananta kai hare-haren wuce gona da irin masarautar Saudiyya kan garin Ta'az ita ce daukan fansa kan gagarumar nasarar da sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa-kai na kasar suka samu na halaka tarin sojojin hayar Saudiyya da suka fito daga kasashen Larabawa daban daban a farkon wannan mako.

Add comment


Security code
Refresh