An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 23 March 2016 04:06

An Dage Gudanar Da Zaman Sulhu A Kasar Mali

An Dage Gudanar Da Zaman Sulhu A Kasar Mali
An dage zaman sulhu da aka shirya gudanarwa a kasar Mali a tsakanin gwamnati da kuma bangaren 'yan tawaye har sai abin da hali ya yi.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoto daga birnin Bamako cewa, Fahad Ag Almahmud jagoran daya daga cikin bangarorin 'yan tawaye da suke dauke da makamai a rewacin Mali yana cewa, an dage zaman taron da aka shirya gudanarwa tsakaninsu da gwamnati a ranar 27 zuwa 30 ga wannan wata na Maris, har zuwa wani lokaci nan gaba.

A cikin watan Yunin 2015 da ta gabata ce dai gwamnatin Algariya ta jagoranci tattaunawa a tsakanin bangarorin gwamnatin Mali da kuma 'yan tawaye, inda aka sa hannu kan yarjejeniyar sulhu, duk kuwa da cewa masu sanya ido na majalisar dinkin duniya sun ce an samu keta yarjejeniyar a wasu yankuna na arewacin kasar ta Mali.

Add comment


Security code
Refresh