An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 22 March 2016 04:49

An kori Alkalai masu goyoyn bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a Masar

An kori Alkalai masu goyoyn bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a Masar
Ma'aikatar shara'a ta kasar Masar ta kori Alkalai 15 masu goyon bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a jiya Litinin.

Wannan mataki na daga cikin yunkurin da magabatan Alkahira ke yi na kawo karshen magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar, wata Majiyar shara'ar kasar ta ce an dauki wannan mataki ne bayan zaman kwamitin Ladabtarwa na alkalan ya zauna, inda ya gudanar da bincike mai tsanani tare da tabbatar da cewa wannan alkalai 15suna sanya siyasa a aikinsu, wanda kuma hakan ya sabawa aikin alakali.

Har ila yau majiyar ta ce Majalisar koli ta Ladabtar da alkalai ta dage zaman hukumata wasu alkalai 55 na daban zuwa ga ranar 28 ga watan Maris.

wadannan alkalai 15 da aka kora da ma wasu alkalai da dama na daga cikin alkalan da suka hade da kungiyar alkalai mai lakabin Alkalai saboda Masar, da tun bayan zanga-zangar da Al'ummar kasar ta yi da ya kawo karshen Gwamnatin Husni Mubarak a shekarar 2011 suka goyawa kungiyar 'yan uwa musulmi baya.

Add comment


Security code
Refresh