An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 22 March 2016 03:11

Damuwar Banki Moon Kan Rashin Samun Mafitar Siyasa A D/Congo

Damuwar Banki Moon Kan Rashin Samun Mafitar Siyasa A D/Congo
Babban saktaren MDD Banki Moon ya bayyana damuwarsa kan yadda aka kasa samun mafuta ga harakokin siyasar kasar

Kamfanin dillancin Labaran Kasar Faransa daga birnin New York ya nakalto Banki Moon cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban kwamitin tsaro na MDD jiya Litinin ya sake kira ga dukkanin bangarorin siyasar kasar D/Congo da su magance sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa, da hakan shi zai sanya a shirya zaben da kowa zai amince da shi bisa dokar kundin tsarin milkin kasar.

A watan Nuwamba mai zuwa ne ya kamata a gudanar da zaben na Congo, amma a kwai yuyuwar dagesa saboda sabanin dake tsakanin jam'iyun siyasar kasar.

Gungun jam'iyun adawa na shugaba Josep kabila wanda ke rike da madufun ikon kasar tun a shekarar 2001 sun zarke shi da kokarin yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima da zai bashi dama sake tsayawa takara a zaben da ake shirye-shiryen gudanarwa.

Add comment


Security code
Refresh