An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 19 March 2016 19:31

Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Akalla 9 A Kasar Iraki

Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Akalla 9 A Kasar Iraki
Mahukuntan Iraki sun sanar da mutuwar mutane akalla 9 tare da jikkatan wasu fiye da 20 na daban sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai a wasu yankunan kasar a yau Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa; Wani bom ya tashi a kusa da wata kasuwa a kauyen Mahmudiyya da ke kudancin kasar Iraki, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 2 tare da jikkatan wasu 7 na daban.

Har ila yau wasu 'yan bindiga dadi sun kai harin wuce gona da iri kan wani gida a kauyen Mada'in da ke kudancin kasar, inda suka kashe mutane akalla 6 iyalan gida guda.

Haka nan wani tashin bom a yankin Hayyul-Amal da ke kudu maso yamma da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki ya lashe ran mutum guda tare da jikkata wasu adadi masu yawa.

Add comment


Security code
Refresh