An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 19 March 2016 18:16

Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Janye Sojojinta Daga Kan Iyakar Kasarta Da Sudan

Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Janye Sojojinta Daga Kan Iyakar Kasarta Da Sudan
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauki matakin janye sojojinta da ta jibge a kan iyakar kasarta da makobciyarta Sudan.

Wani babban jami'in kasar Sudan ta Kudu da ya bukaci a sakaye sunansa a yau Asabar ya bada labarin cewa; Matakin da sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu suka dauka na janyewa daga kan iyakar kasar da Sudan ya zo ne a bayan umurnin da shugaban kasar Silva Kirr ya bayar na kawo karshen zaman dardar tsakanin kasarsa da makobciyarta sudan tare da fatar ganin an samu gudanar kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu.

Har ila yau wasu rahotonni suna bayyana cewa; Matakin da gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauka na janye sojojinta daga kan iyakar kasarta da Sudan ya zo ne bayan da mahukuntan SUdan suka yi gargadin rufe kan iyakar kasarsu da Sudan ta Kudu kan zargin gwamnatin Sudan ta Kudu tana taimakawa 'yan tawayen Sudan da suke yankin Darfur, Blue Nile da kuma Kordofan ta Kudu.

Add comment


Security code
Refresh