An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 18 March 2016 04:31

De Mustura:An tattauwa tsakanin Gwamnatin Siriya da 'yan tawayen kan masayan Fusunoni.

De Mustura:An tattauwa tsakanin Gwamnatin Siriya da 'yan tawayen kan masayan Fusunoni.
Wakilin MDD na musaman kan kasar Siriya ya bayyana cewa mun tattauna da tawagar Gwamnatin Siriya da kuma na 'yan Adawa mazauna birnin Riyad kan batun masayar firsunoni

A wani taron Manema labarai da ya gabatar jiya a birnin Ganeva, Stephen De Mustura wakilin MDD na musaman kan kasar Siriya ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a tattaunawar Sulhu da ake ci gaba da yi tsakanin Gwamnatin Siriya da bangare 'yan adawar kasar, inda ya ce ya zuwa yanzu an cimma matsaya kan mahiman batutuwa tsakanin bangarorin biyu.

De Mustura ya ce wannan kyakyawan sakamako da aka samu na zuwa ne sanadiyar ci gaba da mutunta yarjejjeniyar tsagaita wuta a kasar.

A bangare guda De Mustura ya tabo batun Agajin gaggauwa, inda ya ce ya zuwa yanzu an kai Agajin gaggauwa ga wasu yankunan kasar, amma har yanzu wasu yankunan da suke cikin tsakanin bukata ba a kai masu agajin ba, kuma ya zama wajibi a gaggauta kai musu Agajin domin kubutar da su daga hallaka.

Tun a ranar Litinin din da ta gabata ce aka fara tattaunawar sulhun tsakanin tawagar Gwamnatin Siriya da kuma ta 'yan tawaye bisa shiga tsakanin Stephen De Mustura wakilin MDD na musaman kan kasar Siriya a birnin Ganeva.

Add comment


Security code
Refresh