An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 18 March 2016 03:13

MDD ta yi Alawadai da Harin ta'addancin da a kai A Najeria

MDD ta yi Alawadai da Harin ta'addancin da a kai A Najeria
Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai cikin Masallaci a jihar Borno dake arewa masu gabashin Najeria.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa a jiya Alkhamis, Banki Moon ya bayyana damurwa a kan harin Bom din da ake tsamanin 'yan boko haram ne suka kai shi cikin wani masallaci dake gefen garin Maiduguri na jihar Borno da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 25 yayin da wasu 30 na daban suka jikkata.

Yayin da yake bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata, Banki Moon ya bukaci Gwamnatin Najeria da ta bada himma wajen kula da lafiyar wadanda suka jikkata sanadiyar wannan hari.

A ranar Larabar da ta gabata ce wasu mata biyu sanya da kayan maza suka kai hari kunan bakin wake a wani masallaci dake gefen birnin Maiduguri na Jihar Borno, yayin da Al'ummar musulci ke sallatar Asubahi.

Wannan hari dai shine irinsa na biyu da aka kai arewa maso gabashin kasar ta Najeria cikin wannan wata na Maris da muke ciki.a cikin wata favrayun da ya gabata an kai hare-hare a yankin har so 4, yayin da a watan janairun da ya gaba ce shi aka kai so 8, hakan kuwa shi ke nuna cewa matakan da gwamnati ke dauka yana samun nasara, idan aka yi la'akari da raguwar kai harin cikin ko wani wata.

Add comment


Security code
Refresh