An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 17 March 2016 05:44

Kungiyar Palasdinawa Ta Hamas Ta Yi Kakkausar Suka Kan Mahmud Abbas

Kungiyar Palasdinawa Ta Hamas Ta Yi Kakkausar Suka Kan Mahmud Abbas
Kungiyar Palasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka kan shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar Palasdinawa Mahmud Abbas Abu-Mazin Kan yadda yake gudanar da shugabancin hukumar ta Palasdinawa.

Salah Al-Bardawil daya daga cikin manyan jami'an kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas a jiya Laraba ya yi dirar mikiya kan bakar siyasar shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa Mahmud Abbas Abu-Mazin yana mai zarginsa da juya akalar shugabancin Palasdinawa zuwa ga fada da kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa da nufin dadada wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da burge ta.

Salah Al-Bardawil ya kuma mai da martani kan furucin shugaban hukumar ta Palasdinawa da ke cewa; ba zai amince da ci gaba da gudanar da gwagwarmaya da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar amfani da makami ba, inda Salah Al-Bardawil ke cewa; Jimawa a kan karagar shugabancin al'ummar Palasdinu ce ta kai Mahmud Abbas ga fara kare munanan manufofin yahudawan sahayoniyya.

Add comment


Security code
Refresh