An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 14 March 2016 11:56

Amnesty Ta Bukaci A Sako 'Yan Adawa A Kasashen Bahrain Da Saudiya

Amnesty Ta Bukaci A Sako 'Yan Adawa A Kasashen Bahrain Da Saudiya
Yayin da take Allawadai kan yadda mahukantar Bahren ke ci gaba da wulakanta 'yan adawa, Kungiyar Kare hakin bil-adama ta MDD Amnesty International ta bukaci a sako daya daga cikin shugabanin 'yan adawar kasar

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, Kungiyar ta bayyana cewa a baya bayan nan gwamnatin kasar Bahren ta tsananta cin zarafin 'yan adawa a kasar kuma ta bukaci da a sako Fadil Abas daya daga cikin shugabanin 'yan adawar kasar da kotu ta yanke masa hukuncin shekaru biyar a gidan Yari.

Har ila yau Kungiyar ta bukaci magabatan Saudiya da su dakatar da zartar da hukunci kisa kan matasan kasar kamar yadda aka yiwa Ali Muhamad Namr matashi dan shekaru 17 a duniya kuma Dan Dan uwan Shekh Nimr Bakir Annimr wanda aka kame bayan da halartar wata zanga-zanga kuma kotu aka yanke masa hukuncin kisa sannan kuma aka zartar da shi.

Add comment


Security code
Refresh