An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 13 March 2016 04:07

Amurka : Dan Bindiga Ya Kashe Mutane Hudu A Chicago

Amurka : Dan Bindiga Ya Kashe Mutane Hudu A Chicago
Wani dan bindiga dadi ya yi barin wuta kan jama'a a jihar Chicago na kasar Amurka, inda ya kashe mutane akalla 4 tare da jikkata wasu goma sha biyu na daban.

Majiyar 'yan sandan jihar Chicago ta kasar Amurka a jiyar Asabar ta sanar da cewa; Wani dan ina ga kisa ya kai hare-haren wuce gona da iri kan yankuna daban daban da ke jihar, inda ya kashe mutane akalla 4 tare da jikkata wasu 12 na daban, kuma mafi yawan mutanen da harin ya ritsa da su tsakanin wadanda suka mutu ko suka jikkata 'yan shekaru kasa da 30 ne a duniya.

 

Matsalar tashe-tashen hankula musamman kai hare-haren wuce gona da iri kan fararen hula ya zame ruwan dare gama duniya a jihar ta Chicago musamman a tsakanin gungun matasa da suke rayuwa a yankuna mafi talauci a jihar.

Add comment


Security code
Refresh