An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 12 March 2016 11:13

Dubban Mutane Ne Suka Rasu A Sudan Ta Kudu

Dubban Mutane Ne Suka Rasu A Sudan Ta Kudu
Rikicin Shekaru biyar na Sudan ta Kudu ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

A cikin wani rahoton da ta fitar jiya Juma'a, kungiyar kare hakin bil-adama ta Majalisar dinkin Duniya ta bayyana cewa tun bayan samun 'yan cin Sudan ta kudu kasar ta fuskanci rikicin kabilanci da na siyasa,lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 250, sannan kuma kusan rabin 'yan kasar sun yi gudun hijra.inda wasunsu suka nemi mafuka a kasashen Uganda, D/Congo da Afirka ta tsakiya.

Rahoton ya ce halin da 'yan gudun hijrar kasar ke ciki a sansanin 'yan gudun hijra na yankin Bambuti dake gabashin Tsakiya afirka abin a tausaya musu ne. har ila yau a kwai 'yan kasar kimanin million 4.6 ke bukatar taimakon gaggauwa a cikin kasar.

Add comment


Security code
Refresh