An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 08 March 2016 12:42

Shahadar Bapalasdiniya

Shahadar Bapalasdiniya
"Yan Sandan H.K.Isra'ila Sun Harbe wata Bapalasdinya

Da safiyar yau talata wata Bapalasdinya ta yi shahada sanadiyyar harbinta da 'yan sandan Yahudawa Su a yi a cikin birnin qudus.

Mai magana da yawun 'yan sandan haramtacciyar Kasar Isra'ila Loba Samry ya bayyana cewa; Matar da shekarunta su ke a tsakanin hamsin, kuma mazauniyar Unguwar Om Toban da ke cikin birnin Qudus, ta kusanci wani mai gadin iyakar tsohon birnin qudus tana kokarin sarinsa da wuka.

"Yan sandan sun harbe ta kamar yadda su ka bayyana.

A cikin watannin bayan nan dai 'yan sanda da sojojin haramtaciiyar kasar Isra'ila sun harbe palasdinawa da yawa bira riya cewa suna kokarin sukarsu da wuka.

Add comment


Security code
Refresh