An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 08 March 2016 05:44

Amurka Ta Sanar Da Hallaka 'Yan Ta'addan Al-Shabab 150 A Somaliya

Amurka Ta Sanar Da Hallaka 'Yan Ta'addan Al-Shabab 150 A Somaliya
Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa ta samu nasarar hallaka sama da mayakan kungiyar 'yan ta'addan nan ta Al Shabab ta kasar Somaliya 150 a wani hari da suka kai musu da jirgin yaki mara matuki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya jiyo ma'aikatar tsaron kasar Amurkan (Pentagon) tana cewa sakamakon wani hari da dakarun Amurkan suka kai wani wajen ba da horon soji ga 'yan kungiyar ta Al-Shabab da ke arewacin birnin Mogadishu, babban birnin kasar Somaliyan, da jirgin sama marar matukin sun sami nasarar hallaka 'yan Shabab din sama da 150.

Sanarwar gwamnatin Amurkan dai ya kara da cewa 'yan ta'addan al-Shabab din suna shirin kai wani babban hari ne a lokacin da aka kai musu wannan harin da kuma tarwatsa su.

Har ya zuwa yanzu dai 'yan kungiyar ta Al-Shabab ba su ce komai dangane da wannan labarin ba. Ita dai wannan kungiyar, wanda wani bangare ne na kungiyar Al-Qa'ida ta yi kaurin suna wajen kai hare-haren ta'addanci a kasar ta Somaliya da makwabta.

Add comment


Security code
Refresh