An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 03 March 2016 19:23

Amurka Ta Jinjinawa Tsohuwar Shugabar Gwamnatin Rikon Kwaryar Kasar Afrika Ta Tsakiya

Amurka Ta Jinjinawa Tsohuwar Shugabar Gwamnatin Rikon Kwaryar Kasar Afrika Ta Tsakiya
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya jinjinawa tsohuwar shugabar gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya kan irin rawar da ta taka a fagen rage kaifin tashe-tashen hankula a kasar.

A ganawarsa da tsohuwar shugabar gwamnatin rikon kwarya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya: Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya bayyana cewa; Catherine Samba-Panza ta taka gagarumar rawa a fagen kwadaitar da bangarorin da suke fada da juna a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar musamman a yarjejeniyar da aka cimma a birnin Brazzaville na kasar Congo a shekara ta 2014.

John Kerry ya kara da cewa; Catherine Samba-Panza ta zame babbar abin koyi a fagen shirya zabuka tare da mika mulki ga zababben shugaba ta hanyar lumana lamarin da zai zame babban misali a kan sauran kasashen nahiyar Afrika.

Add comment


Security code
Refresh