An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 02 March 2016 05:07

An Fara Zaben Fidda Gwani A Jihohi 11 Na Amurka,Trump Da Clinton Na Kan Gaba

An Fara Zaben Fidda Gwani A Jihohi 11 Na Amurka,Trump Da Clinton Na Kan Gaba
Rahotanni daga kasar Amurka na nuni da cewa a daren jiya Talata ne aka fara kada kuri'a zaben fidda gwani mafi girma na 'yan takarar shugabancin Amurka karkashin manyan jam'iyyun kasar biyu, wato Democrat and Republican.

Rahotannin sun ce za a gudanar da zaben fidda gwanin ne da ake kira da Super Tuesday a jihohi 11 don zaban gwaninsu daga cikin 'yan takarar da suka tsaya a manyan jam'iyyun biyu, wanda kuma ke zama muhimman zabe ga makomar 'yan takarar neman shugabancin kasar a babban zaben fidda gwani na jam'iyyu wanda za a gudanar a watan Yuli mai zuwa.

A jam'iyyar Republican dai Donald Trump, wanda yake kan gaba shi ne ake sa ran zai lashe mafi yawa daga cikin wadannan jihohin. Alhali a jam'iyyar Democrat kuwa, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurkan Hillary Clinton ce ke kan gaba.

Da dama dai suna ganin wannan zaben a matsayin zakaran gwajin dafin 'yan dangane da makomar 'yan takaran da kuma irin rawar da jam'iyyun za su taka a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba mai zuwa don maye gurbin shugaba Barack Obama na kasar.

Add comment


Security code
Refresh