An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 February 2016 16:47

Banki Moon yayi Alawadai game da ta'addancin Saudiya A Yemen

Banki Moon yayi Alawadai game da ta'addancin Saudiya A Yemen
Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakausar suka kan yadda kawance Saudiya ke ci gaba da kashe fararen hula a kasar Yemen.

Tashar Telbijin din Press Tv wacce ke watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Babban saktaren MDD Bankin Moon cikin wani bayyani da ya yi a yau Litinin ya yi alawadai kan lugudar wutar da jiragen yakin kawancen Saudiya suka yi jiya Lahadi a birnin sana'a fadar milkin kasar yemen.

A cewar Banki Moon, daga watan Satumbar shekarar 2015 din da ta gabata zuwa yanzu , hare-haren da masarautar saudiya ke kaiwa a kasar Yemen yayi sanadiyar hallaka fararen hula da dama.

Har ila yau babban saktaren MDD ya bayyana damuwar kan yadda Saudiya ke ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa tare kuma da yadda gumurzu ke kara tsananin tsakanin 'yan kasar a yamen.

A jiya Lahadi ne jiragen kawancen Saudiya suka yi lugudar wuta a wani babban shago dake arewacin birnin Sana'a, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar fararen hula 32 daga cikin su a kwai Mata da kananen yara tare kuma da jikkata wasu 41 na daban.

Add comment


Security code
Refresh