An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 27 February 2016 05:26

An bukaci da a dakatar da sayarwa saudiya makamai

An bukaci da a dakatar da sayarwa saudiya makamai
Kungiyar Amnesty International ta bukaci da a dakatar da sayar wa kasar Saudiya makamai cikin gaggawa.

A wata Sanarwa da ta fitar jiya Juma'a kungiyar kare hakin bil-adama ta Duniya wato Amnesty International ta bayyana cewa ta nada kwararen hujojji dake nuna cewa Saudiya na amfani da makaman kare dangi wajen kai hare-haren wuce gone da iri kan Al'ummar kasar Yemen.

Kungiyar ta tabbatar da cewa za ta mika wannan bukata ga kasashen Duniya cikin zaman da su yi na bincike kan cinikin makamai ranar 29 ga wannan wata na Fabrairu da muke ciki.

A ranar 16 ga watan Janairun da ya gabata kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa ta nada hujjoji dake nuna cewa kasar Saudiya ta sake amfani da makaman kare dangi a ruwan bama-baman da ta yi kan Al'ummar Sana'a fadar mulkin kasar yemen.

A makon da ya gabata ma, kungiyar tarayar Turai ta amince da wani kudiri na dakatar da sayar wa saudiya makamai.

Add comment


Security code
Refresh