An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 16 February 2016 05:48

Kwamitin Tsaron MDD Zai Tattauna Batun Harin Turkiyya Kan Kurdawan Siriya A Yau

Kwamitin Tsaron MDD Zai Tattauna Batun Harin Turkiyya Kan Kurdawan Siriya A Yau
A wani lokaci a yau din nan Talata ne membobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai su gudanar da wani zama na sirri don tattauna batun hare-haren soji da kasar Turkiyya take kai wa Kurdawan kasar Siriya a cikin kasar ta Siriya.

Rahotanni sun bayyana cewar kasar Rasha , wacce take da kujerar dindindin a kwamitin tsaron ne ta bukaci a gudanar da wannan zaman don tattaunawa wannan batu na ci gaba da kai hare-haren da sojojin Turkiyya suke kai wa Kurdawan kasar Siriya a arewacin kasar lamarin da ake ganin yana iya kara dagula lamurran tsaro a yankin.

Tun kwanaki ukun da suka gabata ne dai sojojin Turkiyyan suke ci gaba da kai hare-hare kan wajajen da 'yan kungiyar Kurdish People's Protection Units (YPG) suke a arewacin kasar Siriya wai da nufin hana Kurdawan isa garin A'zaz da ke kan iyakar Siriya da Turkiyyan lamarin da kasar Rashan da ma wasu kasashen suke nuna damuwarsu kansa da cewa hakan yana iya zaman abin da zai kara ruruta rikicin kasar Siriyan ganin cewa hakan keta hurumin wata kasa ce mai cin gashin kanta.

'Yan kungiyar ta YPG ta Kurdawan dai suna fada ne da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh ko kuma ISIS a kokarin da suke yi na fatattakansu daga sauran wajajen da suke rike da su a arewacin kasar Siriya lamarin da ya sanya da dama suke fassara wadannan hare-hare na gwamnatinTurkiyyan a matsayin wani taimako ga 'yan kungiyar ta'addancin ta Da'esh da suke ci gaba da shan kashi a hannun Kurdawan.

Add comment


Security code
Refresh