An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 07 February 2016 18:26

Kotun H.K.Isra'ila Ta Daure Dan Majalisar Dokokin Kasar Balarabe A Gidan Kurkuku

Kotun H.K.Isra'ila Ta Daure Dan Majalisar Dokokin Kasar Balarabe A Gidan Kurkuku
Kotu a haramtacciyar kasar Isra'ila ta zartar da hukuncin dauri a gidan kurkuku kan wani dan Majalisar Dokokin Kasar da ke wakiltan Larabawa Palasdinu a Majalisar.

Wata kotun haramtacciyar kasar Isra'ila a garin Nasirah da ke arewacin yankin Palasdinu da aka mamaye a yau Lahadi ta zartar da hukuncin dauri na tsawon watanni shida kan Hunain Za'abi dan Majalisar Dokokin haramtacciyar kasar ta Isra'ila da ke wakiltan Larabawa kan zargin cin mutuncin 'yan sanda tare da cin tararsa na wasu makuden kudade.

Hukuncin daurin zai fara ne bayan shekaru biyu wato bayan karshen wa'adinsa a Majalisar Dokokin kasar saboda a halin yanzu yana da kariya ta kasancewar dan Majalisar Dokoki a Haramtacciyar kasar.

Add comment


Security code
Refresh