An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 03 February 2016 17:58

Palasdinawa Uku Sun Yi Shahada A Birnin Qudus

Palasdinawa Uku Sun Yi Shahada A Birnin Qudus
Wasu 'yan gwagwarmayar palasdinawa uku sun yi shahada sakamakon bude musu wutan bindiga da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a yau Laraba.

Majiyar Palasdinawa ta sanar da cewa; 'Yan gwagwarmayar Palasdinawan uku sun kai harin daukan fansa ne a yankin Babul-A'moud da ke birnin Qudus, inda suka bude wuta kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila lamarin da yayi sanadiyyar jikkatan sojoji hudu kuma halin biyu daga cikinsu ya munana.

Bayan dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu, dukkanin Palasdinawan uku sun yi shahada, kuma mahukuntan yahudawan sahayoniyya sun kafa dokar ta baci a yankin na Babul-A'moud.

Tun bayan bullar Intifadhan Palasdinawa na baya-bayan nan watanni biyar da suka gabata a kokarin da suke yi na kare kansu daga wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida da kuma hurumin masallacin Qudus yawan Palasdinawan da suka yi shahada sun haur 170.

Add comment


Security code
Refresh