An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 01 February 2016 06:42

Shahadar Palasdinawa 22 Tare Da Kame Wasu 460 A Watan Janairu

Shahadar Palasdinawa 22 Tare Da Kame Wasu 460 A Watan Janairu
Wata cibiyar bincike mai zaman kanta a Palasdinu ta bayyana ce; A cikin watan Janairun da ya gabata kacal sojojin Yahudawan Sahayoniyya sun yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa akalla 22 tare da kame wasu fiye da 460 na daban.

Cibiyar gudanar da bincike ta Abdullahi Hawarani a jiya Lahadi ta fitar da rahoton cewa; A cikin watan Janairun da ya gabata na wannan sabuwar shekara ta 2016, Palasdinawa akalla 22 ne suka yi shahada kuma 6 daga cikinsu kananan yara sakamakon hare-haren wuce gona da irin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankunan Palasdinawa.

 

Har ila yau Cibiyar binciken ta tabbatar da cewa; A cikin watan na Janairu Palasdinawa fiye da 460 ne sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra'ila suka yi awungaba da su a yankuna daban daban na Palasdinawa. Baya ga rusa gidaje fiye da 50 na Palasdinawa lamarin da ya kai ga raba Palasdinaa da dama da muhallinsu.

Add comment


Security code
Refresh