An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 30 January 2016 05:56

Palasdinawa 76 Ne Suka Jikkata A Dauki Ba Dadi Da Sojojin H.K.Isra'ila

Palasdinawa 76 Ne Suka Jikkata A Dauki Ba Dadi Da Sojojin H.K.Isra'ila
Dauki ba dadi tsakanin Palasdinawa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya yi sanadiyyar jikkatan Palasdiawa kimanin 76 sakamakon amfani da iskar gas mai guba da harbi da bindiga da sojojin na haramtacciyar kasar ta Isra'ila suka yi a jiya Juma'a.

Ma'aikatar lafiya ta Palasdinawa a jiya Juma'a ta sanar da cewa; Sakamakon dauki ba dadi da aka yi tsakanin al'ummar Palasdinu da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a yankunan da suke yankin Zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan a jiya Juma'a, Palasdinawa 76 suka jikkata bayan da sojojin na haramtacciyar kasar ta Isra'ila suka dinga harba musu iskar gas mai guba gami da harbi da bindiga kan mai uwa da wabi.

Tun daga watan Aprilun shekarar da ta gabata ta 2015 dauki ba dadi tsakanin Palasdinawa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da gudana a kokarin da Palasdinawan ke yi na hana yahudawan sahayoniyya ci gaba da keta hurumin Masallacin Qudus mai alfarma

Add comment


Security code
Refresh