An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 20 January 2016 17:11

Ko Kunsan (1-30) Abaan Shekara ta 1394 Hijira Shamsiyya

Ko Kunsan (1-30) Abaan Shekara ta 1394 Hijira Shamsiyya
Yau Jumma’a 01-Abaan-1394H.SH= 09-Muharram-1437H.K.=23-Octoba-2015M.

Yau Jumma’a 01-Abaan-1394H.SH= 09-Muharram-1437H.K.=23-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Muharram-61H.K. Shimr bin Zil-jaushan daga cikin mayakan Umar bin Sa’ad ya zo wajen haimomin Imam Husain (a) ya kir yayan yarsa Fatima ummul banin matar Imam Ali(a) daga kabilarsa bani Kilab, wato Abbas da yan uwansa Abdullahi, Jaafar da kuma Usman. Da imam Husain (a) ya ji muryar Shimr sai ya cewa Abba ku kiran dan uwanku. Da suka je sai Shimr ya mika masu wata takarda ta amintar da su da sharadin su bar Imam Husain(a) sai Abbas ya ce masa: All.. ya tsinewa amincin da ka samo mana. Ya kai makiyin All..ka amintar da mu amma dan manzon (a) All..bai da aminci? Daga nan sai Yay i fushi ya kada dokinsa ya tafi. A daren ne, wato daren Ashoora Imam Husain (a) ya aiki Abbas kaninsa yay a je ya fadawa Ibn Sa’ad cewa, ya jinkirta masu zuwa gobe da safe don su raya dare da addu’oee da kuma salla suna rokon All…A cikin faren ne Imam Husain (a) ya tashi cikin sahabansa da suka rage tare da shi ya ce masu duk wanda yake so yay i amfani da duhun daren nan ya fice daga nan don gobe da safe ba wanda zai rage da rai cikimmu. Amma sahabbansa sun kara jaddada masa cewa ba zasu tafi su barshi ba.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Octoban-1947M. Aka haifi Dr Abdul’aziz Rantisi shugaban kungiyar Hamas ta Palasdinwa masu yaki da yahudawan sahyoniyya yan mamaya. Dr Rantisi yana dan wattannin 6 a duniya iyayensa suka kaura daga cikin Palasdinu suka kuma garin Khan Yunus a yankin Gaza a lokacin yakin shekara ta 1948M. anan yi girma ya kuma kammala karatun likitanci a kasar Masar. Bayan kisan shugaban kungiyar Hamsa Sheikh Ahmad Yasin. Kungiyar ta mikawa Dr Rantisi shugabancin kungiyar. Amma bayan kwanaki 26 kacal da karban wannan aikin sai yahudawan suka kasheshi tare da wasu masu rakiyarsa suk ukku a lokacinda yake tafiya cikin Motarsa a yankin na Gaza a ranar 7-Afrilun -2004M. yana dan shekara 57 a duniya.

**Masu saurare ko kunsan cewa shekaru 38 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Abaan-1356H.SH. Aya. Sayyeed Musta Khomaini (q) babban dan Imam Khomaini wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran yay i shahada. An haifi Aya. Musta a birnin Qum a shekara 1309 H.K. Bayan kammala karatun Primari ya shiga Nauza inda ya ci gaba da karatun har ya kai ga matsayin mujtahidi yana dan shekara 27 a duniya. Saga nan ya fara karantarwa, Aya. Mustafa ya kasance tare da mahaifinsa Imam Khomaoni a duk tsawon lokacin gwagwarmaya da Tagood. Amma a rana irin ta yau a birnin Najaf na kasar Iraqi jami’an tsaron sarki sha tare da samun taimakin na Iraqi suka kashe shi a cikin gidansa.

==================================================================.

Yau Asabar 02-Abaan-1394H.SH=10-Muharram-1437H.K.=24-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato.10-Muharram-61H.K. Daya daga cikin yake yake mafi sosa rai ya auku a kasar Karbala na kasar Iraqi. Inda Husain bin Ali (a) jikan manzon All..(s) ya tare da sahabbansa wadanda basu fi 72 ba suka shiga yaki tare da rundunar Yaizi dan mu’awiya wadanda suka kai kimanin mayaka dubu 20 auwa saba. An fara yakin ne tun safe har zuwa bayan azzahar inda aka kashe dukkan sahabbansa. Aka kuma kama sauran yara da mata wadanda da dama daga cikinsu jikokin manzon All…(s) ne. a matsayin bayi. Sadaukar da rai wanda Imam Husain (a) yayi a Karbala shi ne ya farkad da al-umma kan mummunan halin da Musulunci ya dasa ciki karkashin azzaluman shuwagabanni.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1370 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Muharram-67H.K. Ubaidullahi Bin Ziyad Walin Kufa wanda shirya kisan Imam Husain (a) da sahabbansa a Karbala a shekara ta 61 H.K. ya halaka a hannun mayakan Mukhtar Athaqafi masu Dakar fansa kan wadanda suka kashe Imam Husain (a) da sahabbansa a Karbala. Shekaru 6 bayan waki’ar Karbala Rundunar Mukhtar athaqafi sun kara da na Sarki Abdulmalik bin Marwan a kusa da garin Musil na kasar Iraqi inda suka kashe sojojin bani umayya kimani dubu 70. A lokacinda suka ga cewa an rinjayesu sai Ubaidullah ya so ya gudu amma Ibrahim dan Malikul Ashatar ya bishi dai da ya halaka shi. Har’ila yau a wannan yakin ne aka kashe Shimr bin zi-ljaushan wanda ya yanka kan Imam Husain (a) a ranar karbala.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Muharram-1415H.K. Munafukai makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun tada wani Bom a cikin haramin Imam Rida (a) dake birnin Mashad a arewa maso gabacin kasar Iran. Bom din ya tashi ne a ranar Ashoora wacce ta yi dai dai da ranar 30- Khurdod-1373H.SH, a dai lokacinda musulmi masoya iyalan gidan manzon Al…(s) suke makokin Ashoora a harami na limani na 8 daga cikin limamai masi tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s). Da dama daga cikin masoya sun rasa rayukansu ko kuma suka ji rauni.

========================================================.

Yau Lahadi 03-Abaan-1394H.SH=11-Muharram-1437H.K.=25-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Muharram-61H.K. Ayarin iyalan Imam Husain (a) wadanda mayakan Yazid suka kama a matsayin fursinonin yaki a Karbala sun kama hanyar kasar Sham inda cibiyar mulkin bani umayya take. A wannan karin Imam Aliyu Zainul Abidina (a) da ammarsa zainab (s) ne suke jagorantar wannan ayarin. Idan kaga iyalan gidan manzon All..(s) a wannan ayarin , zakaga cewa babu wata karayar zuciya ko tsoro tattare da su bisa mummunan halin da suke ciki suna gani su ne da nadara. Banda haka tattare da ayarin akwai kawukan mayakan karbala wadanda sojojin yazid suka yayyanka suka rabasu da jikunansu suka dora su kan masuna.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 98 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Octoba-1917M. Yumkurin mutanen kasar Rasha na ganin bayan azzaluman sarakunan kasar ya kai ga nasara, kuma jam’iyyar gurguzu ta kama madafun iko da kasar. Kafin haka dai zaluncin da sarakunan Rasha suke wa mutanen kasar ya kai ga talakawa kama daga manoma da kuma ma’aikata duk sun shiga cikin wannan yunkurin da kauda zalunci a kasar. Mabiya jam’iyyar gurguzu sun kama dukka manya manyan cibiyoyin kasar sun kuma shelanta tsarin gurgucia a matsayin tsarin mulkin kasar. Sai dai bayan shekaru 70 da kafa tsarin gurguzu a Rasha da kuma tarayyyar Soviet tarayyar ta rushe a shekar 1991M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 92 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Abaan-1302H.SH. Sarki Ahmad Sha Qajar na karshe daga cikin sarakunan kajarawa ya nada Rida Khan Mir-Panj a matsayin Priministan kasar Iran. Sannan bayan mako guda da nada shi yay i tafiya zuwa kasashen Turai. Fitansa daga cikin kasar ke da wuya Rida Pahlawi ya fara sauye sauyen a gwamnatin kasar. Sannan a hamkala a hankali ya hana sankin dawowa gida sannan ya nada kansa a matsayin sarkin Iran.

Sarkin Ahmad da kansa ya san cewa idan ya fita daga kasar a lokacin bai san cewa zai dawo ko ba zai dawo ba. da haka kuma Dangin Palawi suka fara mulkin kasar Iran.

===================================================.

Yau Litinin 04-Abaan-1394H.SH=12-Muharram-1437H.K.=26-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Muharram-61H.K. Ayarin Fursinonin Karbala wadanda suka hada da mata da marayun shahidan Karbala ta isa birnin Kufa a fadar Ubaidullahi bin Ziyad. Imam Sajjad (a) da ammarsa Zainab (s) sun eke jagorantar wannan ayarin, duk tare da wahalhalun da suke sha a hannun sojojin yazid dan Mu’awiya shuwagabannin ayarin sun aiwatar da wazifarsu a gaban azzaluman sarakuna bani umayya. Sannan sun bayyanwa mutanen kufa laifin da suka yin a kwale Imam Husain (a) tare da azzalumai basu tallafa masu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Muharram-61H.K. A rana irin ta yau ce aka bizne gawaki masu tsarki na shahidan karbala. Bayan waki’ar Karbala a ranar 10 ga watan Muharram sojojin yazid sun raba gawakin da kawukansu sun tafi da su sannan sun yayyanka jikunkunansu ta yadda ba wanda zai iya gane su. Sannan ba wanda yake da jur’a na bizne gawakin sai da matan kabilar bani asad da suke kusa da wurin suka aibata mazazensu, da rashin binzne gawakin. Sannan suka zu wurin amma kuma suka kasa bambanta gawakin. Anan ne Imam Sajjad (a) da karamarsa ya halarto wurin inda ya fayyace masu gawakin suka bizne ko wane inda ya dace.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1342 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Muharram-95H.K. Bisa wasu ruwayoyi a rana irin ta yau ce Imam Aliyu bin Husain (a) wanda ya shahara da Zainul abideen yay i shahada. Imam Sajjad (a) ya halarci yakin Karbala, amma kasancewa bai da lafiya bai yi fito na fito da sojojin yaziz ba. Imam sajjad (a) tare da sauran iyaln gidan manzon Al..(s) sun rayu a cikin rayuwa mai wahala bayan yakin karbala. Amma duk da haka ya tarbiyantar da malmai sun kai 170, sannan ya bar mana ilmi a bangarorin ilmi da dama daga cikinsu akwai addu’oe da suke cikin littafin sahifatussajjadiyya.

===============================================.

Yau Talata 05-Abaan-1394H.SH=13-Muharram-1437H.K.=27-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Muharram-61H.K. Abdullahi bin Afif daya daga cikin masoya iyalan gidan manzon Al…(s) a garin Kufa ya yi shahada. Bayan shigowar ayarin iyalan gidan manzon All..(s) garin Kufa da kuma wulakancin da walin kufar Ubaidullahi bin Ziyad yayi masu. Abdullahi bin Afif ya kasa hakuri ya tashi a cikin masallaci ya mayarwa walin na Kufa marta wanda ya fusatar da shi. Amma don kariyar da ya samu daga kabilar an kasa kamashi da rana sai da dare jami’an tsaron walin suka shiga gidansa suka kashe shi da saran takobi a rana irin ta yau. Shi ne shahidi na farko bayan waki’ar karbala.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 57 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Octoba-1958M. Janar Muhammad Ayyub Khan, mataimakin shugaban kasar Pakistan ya yi wa shugaban kasar na lokacin Eskandar Mirza juyin mulki wanda ba’a zubar da jinni ba. Wannan juyin mulkin ya auku ne shekaru 11 da samun encin kai na kasar Pakistan. Shuga Ayyub Khan ya gudanar da zabe a shekara ta 1965m inda ya lashe shi, sai dai bayan takurawa na yan adawa bayan shekaru 11 da mulki ya sauka ya mika mulki da wani surukinsa mai suna Janar Yaya khan. A shekara 1969M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 42 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Abaan-1352H.SH. Aya. Sayyeed Ahmad Zanjani ya rasu. An haifi Aya. Zanjani a shekara ta 1269H.SH. ya kuma kammala karatun sharar fage a mahaifarsa. Bayan haka ya je birnin Qum inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai wadanda suka hada da Aya. Abdulkarin Ha’iri yazdi. Bayan rasuwar Aya. Ha’iri ya zama babban limamin masallacin makarantar Faiziyya a birnin Qum. Aya. Yazdi ya barman littafai da dama daga cikinsu akwai : اربعین، اَفواهُ الرِّجال، فروقُ الاحکام da wasu da dama.

==================================================================.

Yau Laraba 06-Abaan-1394H.SH=14-Muharram-1437H.K.=28-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Octoba-1962M. Nikita Khrushchev tsohon shugaban tarayyar Soviet ya bada umurni ga jiragen yakin kasar dauke da makaman nuklia a kusa da gabar ruwan Amurka da su dawo gida. Wannan ya kawo karshen rikicin cacan baki da ta taso tsakanin Amurka da tarayyar ta Soviet a lokacin. Kafin haka dai tarayyar Soviet ta girka makaman linzami wadanda aka dorawa makaman nuklia a kasar Cuba wacce take kilomita 90 kacal da kasar Amurka. Wannan ya sa Amurka ta yi barazana jefa makaman nuklia a kan kasar Cuba, sannan tarayyar Soviet ma ta maida martani kan cewa zata cilla makaman nuklia kan Amurka. Amma bayan wannan umurnin hankalin kowa yan kwanta tsoron fadawa cikin yakin nuklia tsakanin kasashen biyu ya kau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 42 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Octoba-1973M. Taha Husain wani kwarerren marubu dan kasar Masar ya rasu. An haifi Taha Husain a wani kauye a kasar ta Masar a shekara 1889M. Shi ne da na 6 a gidansu yana dan shekara ukku ya makance, amma Al.. ya bashi kwakwalwan fahinta. Ya haddace alkur’anin tun yana karami. Ya sami shiga jami’an al-azhar yana dan shekara 14 a duniya. A shekara 1914 ya sami shahadar duktora. A shekara ta 1959 ya sami kyautar kasar Masar don korewarsa a adabin larabci. Kafin ya rasu a shekara 1973 Taha Husain ya rubuta littafai da dama a fannin Adabi Tarihi tafsiri da sauransu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Abaan-1360H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya maida martani mai zafi ga yerima Fahad dan Abdulaziz na kasar Saudia Kan shawarar da ya bayar na amincewa da halaccin kasar Israel don a kawo karshen rikicin larabawa da ita. Imam Khomaini (q) ya fadi a cikin raddin nasa yana cewa “ Da ni da sauran musulmi wajibi ne a garemu mu yi watsi da shawarorin Sadad da kuma Fahdu, kuma wajibe ne mu yi haka don ba abinda mai rauni zai afmana da shi a cikinsu…:

========================================================.

Yau Alhamis 07-Abaan-1394H.SH=15-Muharram-1437H.K.=29-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 848 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Muharram-589H.K. Aka haifi Aliyu bin Musa bin Jaafar wanda aka fi saninsa da sayyed ibn Tawoos a garin Hilla na kasar Iran. Ibn Tawoos ya fara karatu a mahaifarsa sannan ya je birnin Bagdaza inda ya kammala karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa. Ibn Tawoos daga baya ya zama babu wani malamin da ya fishi ilmi a zamaninsa. Ya kuma rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai littafi mai suna «اللهوف». Kan waki’ar Karbala. Ibn Tawoos ya rasu a shekarata 664 H.K. yama dan shekara 75 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 92 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Octoban-1923M. Mustafa Kamal Pasha, wanda aka fi saninsa da Ataturk yay i watsi da tsarin Musulunci ya kuma kafa tsarin da ba ruwansa da addinin a kasar Turkiyya. Bayan yakin duniya na biyu ne turawa suka yayyanka daular usmaniya bayan shekaru 623 tana iko da daula mafi girma a duniya zuwa kasar Turkiya kadai. Sannan shi ma a shekara 1923M Mustafa Ataturk ya mayeshi da tsarin da ba ruwansa da addinin. Yay i kokarin sauyi shi da al’adun turawan yamma. Ko bayan mutuwarsa a shekara ta 1938M an ci gaba da wannan tsdarin . wanna bai hana cewa mafi yawan mutanen kasar Turkiyya musulmin ne ba. Kuma a halin yanzu masu kishin addini suna farfadowa a kasar.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 89 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Abaan-1305H.SH. Aya. Sayyed Hassan Mudarris, wani babban malami kuma dan siyasa a nan kasar Iran yay i shahada. Aya. Mudarris yana daga cikin malamai da suka wayar da kan mutanen kasar Iran kan matsalolin sarakunan Palawi a nan kasar Iran. Da wannan dalilin ne sarki Rida Pahlawi ya tilasta masa gudun hijira ya kuma sa aka kashe shi a rana irin ta yau. Mudarris ya taba zama dan majalisar dokokin kasar Iran.

=======================================================.

Yau Jumma’a 08-Abaan-1394H.SH=16-Muharram-1437H.K.=30-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 176 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Muharram-1260H.K. Turawan Faransa yan mulkin mallaka sun kama shugaban masu gwagwarmaya da su a kasar Algeria Amir Abdulkadir Jaza'iri bayan gwagwarmaya na shekaru 15. Daya daga cikin dalilan da suka sa turawan suka kama Jaza'iri shi ne, bai da sansani cikin kasar Algeria. Don haka yana amfani da kan iyakokin kasar da kasar Morocco ne wajen yakar turawan. Sannan ita kasar Morocco ma tana karkashin ikon turawan Faransa ne, don haka sarkin kasar Morocco ya kore shi daga cikin kasar. Amir Abdulkadir ya share shekaru 9 a gidan kason turawan Faransa sannan suka sake shi da sharadin kada ya sake komawa kasar Algeria.

**Masu saurar ko kun san cewa shekaru 105 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Octoba-1910M. Henri Dunant mutumin da ya kafa kungiyar bada agaji ta red cross ya rasu. An haifi Henry a shekara ta 1828M a birnin Vienna na kasar Austria. Henri ya kafa kungiyar red Cross ne bayan da ya ga yake yake sun yawaita a yankin kasashen turai. Kafin haka dai Hinre ya rubuta wani karamin littafi in da ya bayyana manufar kafa kungiya ya kuma rarraba shi cikin mutanen kasarsa a shekara ta 1968M. A cikin littafin Henri ya bayyana bukatar samar da mutane masu sa kai don tallafawa marasa lafiya, ko wadanda suka ji rauni a yaki ko kuma sanadiyyar sauran musibu.

Daga karshen a cikin watan mayun shekara ta 1863 M aka gudanar da taron kasa da kasa inda kasashen 16 na turai suka halarce shi. Sannan a shekarar da ta biyo wato a ranar 22-Augustan shekara 1864 aka kafa kungiyar Red Cross a taron birnin Vienna. Henri ya karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekara ta 1910M. sai kuma a ranar 30-Octoban-1910M ya rasu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Abaan-1359H.SH. Mohammad Hassan Fahmeede yaro dan shekara 13

A duniya yay i shahada a dai dai lokacinda kasar Iraqi ta mamaye wasu yankuna na kasar Iran. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMi ya kira shi da cewa shi ne shugabammu don raya aikin da ya yi wanda ya akishi ga shahada don kare kasarsa.

Da wannan dalilin ne aka sanya ranar 08 ga watan Abaan na ko wace shekara a matsayin ranar matasa a kasar Iran. Jagoran juyin juya halin musulunci na yanzu Aya. Sayyeed Aliyu Al-khaminaee ya bayyana muhimmanci raya wannan ranar ga matasa musamman wadanda suke dai dai da shekarunsa.

========================================================

Yau Asabar 09-Abaan-1394H.SH=17-Muharram-1437H.K.=31-Octoba-2015.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 484 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Muharram-953H.K. Aka haife Baha'uddeen Amula, wanda aka fi saninsa da Sheikh Baha'ee a garin Ba'alabak na kasar Lebanon. Mahaifinsa babban malami ne a kasar ta Lebanon. A lokacinda zai kaura zuwa kasar Iran ya taho tare da dansa Baha'uddeen. Sheikh Bahaee ya zama babban malami tun yana matashi. Sannan ya rubuta littafai kimani 88 daga cikinsu akwai «جامع عباسی»، «کشکول». Kan hadisai. Sheikh al-bahaee ya rasu a shekara ta 1030H.K.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Octobar-1956M. Kasashen Britania da Faransa sun fadawa kasar Masar da yaki bayan da shugaban kasar masar na lokacin jamal Abdunnasir ya shelanta cewa mashigar ruwa ta Swiz ta zama mallakin kasar. Kafin haka dai wani kamfani mallakar kashen britania ta Faransa ne suke kula da mashigar. Daga baya HKI ma ta shiga yakin. Sai daga karshen an tsagaita bude wuta, sannan MDD ta shiga tsakani inda aka tabbatarwa kasar Masar mallakar mashigar ruwan ta Swiz. A lokacin yakin dai HKI ta mamaye yankin hamadar Sina na kasar Masar.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Octoba-1984M. Wasu masu gadin Priministan kasar India na lokacin mabiya mazhabar addini ta Sik sun kashe ta. A dai dai lokacinda dai, Indira Gandi ta tura jami'an tsaro zuwa ga wurun bautar mutanen sik dake jihar Punjam a tsakiyar kasar don kawo karshen boren da kuma bellewan da suke son yi. Mutanen sik suna da yawan kasha 2% kacal na yawan mutanen kasar India kuma mafi yawansu suna zaune ne a jihar ta Punjam don haka ne suke son ballewa daga kasar India don kafa kasa tasu zalla.

Bayan kisan Indira gandi, dansa Rajib gandi wanda ya gajeta a kan kujerar Priministan kasar shi an kashe shi a wani tashin bom da ya rusta da shi a lokacinda yake yakin neman zabe a wata jiha a kasar.

=====================================================================.

Yau Lahadi 10-Abaan-1394H.SH=18-Muharram-1437H.K.=01-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 128 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Muharram-1309H.K. Aka haifi Aya. Sayyeed Ahmad Khunsari, wanda ya kasance marjaeen taqlidi na mabiya mazhabar shi'a. Aya. Khunsari yana dan shekara 20 a dununiya ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya yi karatu a gaban manya manyna malamai na lokacin wadanda suka hada da Aya. Naeeni, Sayyeed Muhammad Kazim da shareef Esfahani. Bayan kamala Karatu Aya. Khunsari ya dawo Iran inda ya ci gaba da karantarwa a makarantar Hauza ma Aya. Ha'iri a Iraq da kuma Qum. Daga baya an bashi limancin masallacin fayziyya da ke Qum. Sai kuma a shekara ta 1370 ya dawo Tehran inda yak e limanci a masallacin Sayyeed Azizullah. Aya. Khunsari ya ci gaba da wannan aiki a har zuwa karshen rayuwarsa. Amma bayan mutuwarsa an yi masa kabari a Qum.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10—Abaan-1358H.SH. Aya. Sayyeed Muhammad Ali Khadi Tabatabai yay i shahada a hannun wata kungiyar munafukai makiya JMi. An haife shi a shekara ta 1293 H.SH a garin Tabrizi. Ya kammala karatun sharer fage a gida sannan ya koma Qum inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai a birnin Qum wadanda suka hada da Imam Khomani (q) wanda ya assasa JMI. Aya. Tabatabai ya kasance cikin magoya bayan Imam Khomaini (q) a duk tsawon gwagwarmaya da ya yi da Tagutan sarakunan Iran. Sau da dama an daure shi ko kuma an tilasta masa gudun hijira. Bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a nan Iran. Imam ya nada shi wakilinsa a garin Tabriza sannan limamin masallacin jumma'a na garin. Yana cikin wannan aikin ne munafukai suka kashe kashe.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Abaan-1359H.SH. Sojojin Sadam Husain na kasar Iraqi wadanda suke mamaye da wasu yankuna na kasar Iran a lokacin sun sace ministan man fetur na kasar Muhammad Jawad Tandguyon a lokacinda ya kai ziyarar aiki a wasu yankuna masu arzikin man fetur a yankin kudancin kasar. Da farko dai gwamnatin kasar Iraqi ta musanta cewa ta sace ministan amma bayan wani lokaci sun mika gabawansa tare da bayanin cewa ya kashe kansa da kansa a lokacinda suke tsare da shi. Sai dai binciken likitoci sun tabbatar da cewa an azabtar da Muhammad Jawad Tandguyon har ya mutu.

=======================================================.

Yau Litinin 11-Abaan-1394H.SH=19-Muharram-1437H.K.=02-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Muharram-61H.K. Tawagar fursinonin yaki daga iyalan Imam Husain (a) da kuma sauran shahidan Karbala sun kama hanyar Sham daga Kufa bayan mako guda a cikin garin. A cikin mako guda da suka zauna a kofa shuwagabannin tawagar Imam zainul abideen dan Imam Husain (q) da ammarsa Zainab sun nuna jarunta wajen bayyana ta'asar da sarakunan bani umayya suka aikata a karbala da kuma aibata mutanen kufa kan sakacin da suka yi wajen taimakawa Imam Husain (q) da kuma shiga cikin wadanda suka yakeshi, Wannan ya sanya mutanen Kufa suka yi nadama kan wannan sakashin har saida ubaidullahi ya ji tsorom mutanen Kufa zasu yi bori sai ya gaggauta tura fursinonin yakin zuwa sham.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1071 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Muharram-366H.K. Sarki Hasan bin Buwaih daya daga cikin sarakunan dangin Buwaih ya rasu. Sarakunan Buwaih sun yi iko da wasu yankunan kasar Iran daga shekara ta 320H.K. zuwa wani lokaci. Yankunan sun hada da wasu yankuna na kasar Iraqi a halain yanzu har zuwa kan iyakokin kasar sham. Sarakunan wannan dangin sun yi khidimawa addini da ilmi wanda suka hada da nada malamai a matsayin ministoci da kuma kula da harkokin ilmi da raya kasa. Sarki Hassas Bin Bawaih yana daga cikin sarakunan wannan daingin da suka gina makarantu asbitoci da kuma girmama malamai.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 99 da suka gabata a rana irin ta yau wato Sarifu Makka hakiman Makka da Madina ya shelanta kansa a matsayin khalifa a kan dukkan kasashen larabawa. Sharifu makka ya jagoranci tawaye wa daular Usmaniyya da ke da cibiya a kasar Turkiya na yanzu a cikin watan Yuli na wancan shekarar. Turawan ingila sun ingiza Sharifu Makka yay i tawaye ga daular Usmaniya sun yi masa alkawarin za su amince ya zama shugaban kasashen larabawa. A lokacin turawan suna yaki da daular Usmaniya a yakin duniya na daya. Sai dai bayan nasarar da suka samu kan daular Usmaniya turawan basu cika ailkawarin nasu ga sharifu makka. Inda suka goyawa sarki saud masu mulkin saudia a halin yanzu kan sharifu makka. Amma sai suka bawa yayansa mulkin kasashen Jordan da Iraqi daga baya.

=================================================.

Yau Talata 12-Abaan-1394H.SH=20-Muharram-1437H.K.=03-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 107 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Abaan-1287H.SH. Aya. Mirza Hasan Husaini wanda aka fi saninsa da Mirza Khalil ya rasu yana dan shekara 93 a duniya. An haifi Aya. Mirza Hasaini a shekara 1194H.SH. a birnin Najaf na kasar Iraqi. Sannan ya yi karatun shararar fage a gaban mahaifi da kuma yan uwansa. Sanna ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai wadanda suka hada da Sheikh Mohammad Hassan Najafi mai littafin al-jawahir, da Sheikh Murtada Ansari. Bayan ya zama marja'I ya sami mabiya daga kasashen Iran, Iraq, India da Lebanon. Daga karshe Aya. Mirza Hassan Husaini ya zama shugaba hauzan Najaf. Har'ila yau ya rubuta littafai da dama wadanda suka hada da Kitabul Gaiba, da sharhin Najadtul Ibadad. Aya. Mirza Hassan Husain ya rasu yana dan shekara 93 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Nuwamba-1956M. A dai dai lokacinda sojojin HKI suka soma kaiwa kasar Masar hare hare, sojojin yahudawan sun shiga garin Khan Yunus da ke yankin Gaza inda suka kasa mutanen garin 275. Daga cikin wadanda suka kashe akwai sojojin Masar da suke garin, da dukkan majinyata da ke cikin asbitin Khan Yunus, da likitoci da kuma dukkan ma'aikatan jinya a asbitin. Har'ila yau sun je sansanin yan gudun hijira da ke khan yunus suka tada boma suka kashe yara da mata da dama.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekary 42 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Abaan-1352H.SH. Allamah Mirza Abul Hasan sharani daya daga cikin manya manyan malamai a nan iran ya rasu yana dan shekara 71 a duniya. An haufi Allamah Sharani a shekara ta 1281H.SH a birnin Tehran. Bayan kammala karatun sharara fage a nan Tehran Allahmah Sharani ya na dan shekara 26 ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manyan manyna malamai na lokacin wadanda suka hada da Sayyeed Abu Turab Khunsari. Bayan kammala karatu ya dawo nan Tehran inda ya fara karantarwa tarjama da kuma rubuce rubuce a fannonin ilmi da dama. Allah Sharani ya iya harsunan larabci, Faransanci da Ibranci.

=======================================================.

Yau Laraba 13-Abaan-1394H.SH=21-Muharram-1437H.K.=04-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 51 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Abaan-1343H.SH. Jami’an tsaron sarki na sha a nan Iran sun shiga gidan Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Qum, inda suka kama shi suka zo da shi nan Tehran. Sannan ba tare da wani jirkiri ba sun fidda daga kasar zuwa kasar Turkiya. Wannan shi ne masomin gudun hijiransa daga kasar Iran har na tsawon shekaru 14.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau daliban jami’a masu bin tafarkin Imam (q) sun mamaye ofishin jakadancin kasar Iran dake nan Tehran inda suka tabbatarwa duniya cewa ofishin jakadancin wata cibiyar leken asiri na Amurka. Daliban sun kama jami’an diblomasiya kimani 50 a ofishin, tare da amincewar Imam Khomaini (q) sun tsaresu har na tsawon kwanaki 444 a nan Tehran. Wani abin lura a anan shi ne tsare wadannan jami’an diblomasiyyar kasar Amurka ya yi sandiyyar Faduwar jam’iyyar shugaba Jimmy Carter a zaben shugaban kasar Amurca a wancan shekarar.

**Masu sauraro ko kun san cew ashekaru 29 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Abaab- 1365H.SH. Wata jaridar kasar Lebanon ta buga wani labari wanda ya kwaye asirin kasar Amurka kan yakin da sadam Husain ya dorawa kasar Iran da kuma tallafin da gwamnatin Amurka na lokacin take bawa yan tawayen kasar Nicaraguwa. A ranar 14-Yulin-1985 ne wasu mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon suka tilastawa wani jirgi dauke da Amurkawa sauka a Tashar jiragen sama na Beyrut suka ci gaba da tsaresu a cikin jirgin. Wannan ya tilstawa Amurka neman taimakon Iran don warware matsalar. Anan Iran ta bukaci gwamnatin Amurka ta sayar mata makamai, duk da cewa gwamnatin kasar ta dorawa kasar sayarwa Iran Makamai. Amma gwamnatin Ronald Reagan a lokacin ta sayarwa iran makamai masu yawa, amma kuma a dayan bangaren kuma ta ce a mika kudin gay an tawayen Nikaraguwa wadanda suma majalisar dokokin Amurka ta hana a tallafa masu. Bayan wannan fallasar dai da dama daga cikin jami’an gwamnatin Reagan sin ajiye ayukansu.

=========================================================

Yau Alhamis 14-Abaan-1394H.SH=22-Muharram-1437H.K.=05-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 977 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Muharram-460H.K. Sheikh Mohammad Bin Hassan Toosi wanda aka fi saninsa da sheikh Atta’ifa ya rasu. An haifi sheikh Toosi a yankin Toos na arewa maso gabacin kasar Iran a shekara ta 385 H.K. Bayan kammala karatun sharar Fage a gida ya koma birnin Najaf na kasar Iran da zama inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin wadanda suka hada da Allama Mufid da Sayyed Murtada.

A fagen rubuce rubuce kuma Sheikh Toosi ya rubuta tafsirin «التبیان» mai mujalladai 10, sai kuma «تهذیب» و «استبصار» wadanda suka kasance cikin liattafin hadisan manzon Al…(s) da iyala gidansa masu tsarki, kuma suna daga cikin littafin hadisai mazhabar shia mafiya muhimmanci guda 4.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 136 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Nuwamba-1879M. James Maxwell wani masanin ilmin kimiyyar lissafi wanda kuma ya gano wasu dokokin dabi’ar haske da lantaki ya rasu. An haifi James Maxwell a yankin scortland na kasar Britania a ranar 12-Nuwamban-1831M. A shekara ta 1871 James Maxwell ya yada littafinsa na farko kan dokokin dabi’ar haske da kuma kwararar wutan lantarki da maganadisu. Wannan ya maida shi malami mafi sani a bangaren kimiyyar lissafi a jami’an Cambreage. James Maxwell ya rasu a ranar 05-Nuwamban-1879M yana dan shekara 48 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Abaan-1293H.SH. Sojojin kasar Jamus sun mamaye wasu yankuna daga kudancin kasar Iran a dai dai lokacinda ake yakin duniya na daya. A lokacin dai gwamnatin kasar Iran ta dauki matsayin dan ba ruwana a yakin. Amma kasashen Rasha da Daular Usmania basu ji dadin hakan ba, don haka suke mamaye yankin arzadbajan daga arewacin kasar a yayinda kasar Jamus kuma ta mamaye wasu yankuna daga kudancin kasar ta Iran don kare kanta. Wannan halin dai ya jefa kasar cikin matsalolin da dama wadanda suka hada da fari da yiwwa da kuma kisan mutanen da basu san hawa ko sauka ba har zuwa karshen yakin a shekara 1914M.

===================================================================

Yau Jumma’a 15-Abaan-1394H.SH=23-Muharram-1437H.K.=06-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 202 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Nuwamba-1813M. Simon Boliva jarumin kasar Venezuwela wanda ya yunkura don kubutar da mutanen yankin kudancin Amurka daga hannun turawan Espania yan mulkinmallak ya sami nasara a yunkurinsa na farko wajen entar da kasarsa ta haihuwa wato Venezuela. A wannan yankin dai sojojin Simon Boliva 6,500 kacal sun sami nasara a kan sojojin turawan Espania wadanda yawansu ya kai dubu 13. Banyan kasar Venezuela Sojojin Simon Boliva sun entar da kasashen yankin kudancin Amurka da dama daga mulkin mallakar turawan Espania.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 155 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Nuwamban-1860M. Abraham Lincon fitaccen dan siyasar Amurka kuma mai tsananin adawa da bautar da mutane ya zama shugaban kasar Amurka. Bayan hawansa kan kujerar shugabancin kasar an sami rikici tsakanin gwamnatinsa da fararen fata masu goyon bayan bautar da mutane wadanda suke son raba kasar amma daga karshe ya sami nasara a kansu. Lincon ya fara nuna adawarsa da bautar da mutanen tun kafin ya shiga harkokin siyasa a kasar ta Amuka. Amma daga karshe an kashe lincon a shekara ta 1865M da hannun fararen fata masu goyon bayan bautar da mutane musamman bakaken fata.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 140 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Muharram-1297H.K. Allamah Mohammad Mahdi Naraqi daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan kasar Iran ya rasu. Mullah Naraqi ya fara karatu a gida, sannan ya wuce birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatu a gaban manya manyan malamai na lokacin. Bayan kammala karatu ya shiga karantarwa da wallafe wallafen littafai. Daga cikin littafan da Allamah Naraqi ya rubuta akwai «جامع السعادات» wanda ya tattara addu’oe da kuma bayanin halaye masu kyau, sai kuma «انیس الموحدین» wanda ya warware matsalolin akida a cikinsa.

=========================================================

Yau Asabar 16-Abaan-1394H.SH=24-Muharram-1437H.K.=07-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Nuwamba-1956M. Aka kawo karshen yakin mashigar ruwa ta Swiz na kasar masar. A wannan yakin dai kasashen ukku ne suka fadawa kasar Masar da yaki, kasashen sune HKI wacce ta mamaye hamadar Sina na kasar Masar sai kuma kasashen Britania da Faransa wadanda sojojinsu suka mamaye mashigar ruwa ta swiz dake kusa da Port sa’ed. Musabbabin yakin shi ne shelanta mashigar ruwa ta Swiz ta zama ta kasa wanda shugaba Jamal Abdunnasir na kasar masar yayi. Kafin haka dai kasashen Faransa da Britania ne suke kula da mashigar ruwan mai muhaimmanci wacce ta hake taken Malia da kuma tekun medateranian.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Abaan-1357H.SH. Miliyoyin mutanen kasar Iran a duk fadin kasar sun gudanar da zanga zanga don tabbatar da matsayinsu na neman sauyi a kasar duk tare da juyin mulkin sojoji suka yi a kasar Iran a dai dai lokacinda juyin juya halin Musulunci ya kusan kaiwa ga nasara. Manufar juyin mulkin dai shi ne gabatar da wasu sauye sauye na zahira don yaudarar mutane su dawo daga rakiyar Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a wajen kasar a lokacin. Bayan zanga zangar dai Imam ya aike da sako inda ya yabawa mutanen kasar kan goyon bayan da suke bashi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Nuwamba-1985M. Bayan wani juyin mulkin da aka yiwa shugaban kasar Tunisa na lokacin Habib Borgiba, ba tare da zubar da jini ba Zainul-Abideena bin Ali ya zama shugaban kasar ta Tunisia. Habin Borgiba ya zama Priministan kasar Tunisia na farko bayan samun encin kai daga hannun turawan Faransa yan mulkin mallaka a shekara ta 1956M. Sai kuma shekara daya bayan haka ya yiwa sarakin kasar juyin mulkin sannan ya yi watsi da tsarin sarauta. Sai kuma a shekara 1959 ya sauya tsarin mulkin kasar wanda a ciki ya bawa shugaban kasa iko mai yawa a ciki. Daga karshe a shekara ta 1975 ya maida kansa shugaban kasar Tunisia na rai da rai. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1985 bayan shekaru 30 da mulki aka yi masa juyin mulki.

==================================================.

Yau Lahadi 17-Abaan-1394H.SH=25-Muharram-1437H.K.=08-Nuwamba-2015M.

**Masu saurare ko kun sa cewa shekaru 1342 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Muharram-95H.K. Bisa wasu ruwayoyi a rana irin ta yau ce Limami na 4 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s) ya yi shahada. An haifi Imam Aliyu bin Husain (a) wanda ake masa lakabi da Zainul –abidina da kuma Sajjad a garin madina a shekara ta 38 H.K. Bayan shahadar mahaifinsa Imam Husain (a) a karbala a shekara ta 61H.K. Imam Sajjad (a) ya dauki nauyin yada manufar shahadar mahaifinsa a karbala da kuma kare addinin kakaknsa daga kaucewa kan hanyar da ta dace. A wannan tafarkin duk tare da takurawa na sarakunan bani Umayya , Imam Sajjad (a) ya tarbiyantar da tarbiyantar da Dalibai masu yawa wadanda suke karbi sakon Musulunci na asali daga wajensa suka kuma yada shi a duniya. Banda wannan Imam Sajjad (a) ya shahara da halaye masu kyau da kuma yawan addu’a, ta haka ne aka tattara addu’o’insa da ilmin tarbiya a littafi mai suna Sahifatu ssajadiyya.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 120 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Nuwamba-1895M. Wani masanin ilmin kimiyar lissafi dan kasar Jamus mai suna - Wilhelm Conrad Rontgen- ya gano wani haske wanda ya bashi suna x-ray don rashin saninsa kafin hakan. Hasken X-ray dai yana da matukar muhimmanci a ilmin kimiyyar lissafi, inda ake amfani da shi a bangarori da dama daga cikinsu a daular hoton kasusuwan mutane da dabbobi don ratsawa da yake yi cikin jikkuna masu taushi. Wilhelm Conrad Rontgen ya karbi kyautar Nobel a shekara ta 1901M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 62 a rana irin ta yau wato 17-Abaan-1332H.SH. Aka fara shari’ar tsohon Priministan kasar Iran Dr Mohammad Musaddiq, shekaru biyu bayan juyin mulkin da Amurka da Britania suka jagoranta. Laifi na asali da ake tuhumar Dr Musaddiq da shi dai sun shi ne maida kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar Iran ya zama na kasa bayan da turawan Britania suka dade sune kula da shi. Amma a gaban kotun mai gabatar da kara na gwamnati ya gabatar da tuhumar kaucewa umurnin sarki da kyma sabawa sojojin da suka yi juyin mulki. Daga karshe an yanke masa hukunci zama gidan yari na shekaru 3 sannan an ci gaba da tsareshi a gidansa har zuwa mutuwarsa a shekara ta 1345H.SH.

=======================

Yau Litinin 18-Abaan-1394H.SH=26-Muharram-1437H.K.=09-Nuwamba-2015M.

**Masu saurare ko kun sa cewa shekaru 1373 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Muharram-64H.K. Sojojin Yazid dan Mu’awiya sun jefi dakin ka’aba da duwasu sun kuma kona kellensa. Bayan shahadar Imam Husain (a) jikan Manzon All..(s) da kuma kama matansa da yayansa a matsayin fursinonin yaki, al-ummar musulmi sun bayyana kiyayyarsu da sarakunan bani umayya wanda ya kai ga mutane a biranen makka da madina sun kori wali ko gwanonin johohinsu. Bayan haka ne Yazid ya aika da wata runduna karkashin Hassin bin Numai zuwa birnin Makka inda suka kakkashe mutane da dama. Wasu sun nemi mafaka a dakin kaaba amma wannan bai hana sojojin yazid a ranar 14-Muharram -63H.K. jifansu da duwatsu dauke da wuta ba har sai da suka kona dakin suka kashe wadanda suke mafaka a cikinsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 138 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Nuwamba-1877M. Aka haifi Allah Mohammad Iqbal Lahori, masanin ilmin addini a kasar India na lokacin. Bayan kammala karatun sharar fage a gida Allamah Iqbal ya ji kasashen Jamus da Britania don karatun ilmin falsafa. Bayan dawowarsa gida India na lokacin ya fara rubuce rubucen wakoki a fannonin rayuwa da dama. Mafi yawan rubuce rubucensa ya yi su ne cikin harshen Farisanci. Allamah Mohammad Iqbal Lahori ya rasu a shekara 1938M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 26 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Nuwamba-1989M. An rusa bongon balin na kasar Jamus wacce ta rana kasar Jamus da kuma birnin balin kashi biyu bayan yakin duniya na biyu. A karshen yakin duniya na biyu Tarayyar Soviet ta mamaye jamus da gabas a yayinda Amurka Britania da faransa suka mamaye wasu yankuna na yammacin kasar ta Jamus. Amma don sabanin tsarin siyasar da za’a tabbatar a kasar Jamus ya sanya tarayyar Soviet ta gina bongo wacce ta rana jamus da kuma birnin Balin gida biyu. Amma bayan shekaru 28 da raba kasar, jim kadan kafin wargajewar tarayyar Soviet a rana irin ta yau mutanen kasashen biyu suka rusa bongon na Balin wanda ya share fagen sake dunkulewar kasarJamus a cikin watannin da suka biyu baya.

====================================================.

Yau Talata 19-Abaan-1394H.SH=27-Muharram-1437H.K.=10-Nuwamba-2015M.

**Masu saurare ko kun sa cewa shekaru 532 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Nuwamba-1483M. Aka haifi Martin Luther shugaban mazhabar Protestand na kirici a kasar Jamus. Martin ya zama Pastor tun yana matsahi sanna da ya shiga jami’an kuma ya karanci ilmin falsafa wanda ya bude kwakwalsa har ya zama malamin farsafa a jami’an da ya kammala karatu. Daga nan ne Luther ya fara samun sabani da paparoma da wasu manya manyan shuwagabannin mazhabar catholika na lokacin. Da farko ya tarjama Bible zuwa harshen Jamu’sanci sabanin umurnin Paparoma. Sanna a shekara ta 1517 ya fara yunkurin entar da kiristoci Turai daga danniyar shuwagabannin coci da na siyasa a kasashen turai. An shiga yake yaken addinin na lokacin mai tsawo a kasashen Turai musamman a kasar jamus. Daga karshe dai an amince da Mazhabar Protestand. Matine Luther ya rasu a shekara ta 1546M bayan rashin rashin lafiya na karamin loaci.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 40 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Nuwamba-1975M. Babban zauren majalisar dinkin duniya ta samar da wani kuduri mai lamba 3379 wanda ya bayyana akidar sahyoniyya ta yahudawan da suke mamaye da kasar Palsdinu a matsayin akidar wariyar al-umma. Amince da wannan kudurin dai wani babban koma baya ne ga Yahudawan sahyonia. Har’ila yau kudurin ya fusata kasashen duniya da suke goyon bayan haramtacciyar kasar musamman Amurka.

An samar da akidar sahyonia ne a karshen karnin 19 maladiyya, inda kafin haka baya daga cikin akidar yahudawa an cewa su zabubbun Al.. babu kamarsu a dukkan halittun Al… Amma bisa wannan harsashin ne yahudawan sahyonia suka kafa HKi a shekara ta 1948 a kasar palasdinu kuma tun lokacin suke kisa da kuma korari Palasdinawa daga kasarsu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Nuwamba-1981M. Gwamnatin kasar Faransa a cikin kallafeffen yakin da Iraqi ta dorawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kulla cinikin makamai da kasar Iraqi na kudu dalar Amurka billion guda. Tun bayan fara yakin a shekara ta 1980 kasar Faransa take goyon bayan kasar Iraqi. Sannan kafin a kawo karshen yakin kasar Faransa ta sayarwa kasar Iraqi makamai wadanda suka kai kimar dalar Amurka billion 5. Wannan a dai dai lokacinda kasar Iran tana bin faransa bashin kudade dalar Amurka billion guda amma ta ki biya. Makaman da Faransa ta sayarwa Iraqi dai sun hada da Jiragen yaki na zamani, tankunan yaki, makaman linzami da kuma tallafa wajen kera makamai guba.

==================================================================

Yau Laraba 20-Abaan-1394H.SH=28-Muharram-1437H.K.=11-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 97 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Nuwamba-1918M. Aka kawo karshen yakin duniya na daya tare da sanya hannu a yerjejeniyar Armistice. An gudanar da yakin duniya na daya ne tsakanin shekaru 1914-1918M, kuma tsakanin kasashen Jamus da kawayenta wadanda suka hada da ita Jamus, Bulgeria, Daular Usmania , Austria da kuma Hungry a bangare guda, da kuma rundunar hadin guiwa na kasashen Turai da Amurka wadanda suka hada da ita Amurkan, Rasha, Britania, Faransa da kuma Italia a dayan bangaren.

Mutane million 15 suka rasa rayukansu a yakin sannan wasu million 20 kuma suka ji rauni. Har’ila yau an yi asarar dukiyoyi wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka billion 150.

Bayan yakin dai an gudanar da taron Waso, inda aka sanya hannu a kan yerjejeniya ta karshe wacce a cikinta bangaren da suka sami nasara a yakin wato Amurka da kawayanta suka dorawa kasar Jamus wasu sharudda da suka hada da biyan tara, takaida yawan sojojinta da makamanta da kuma takaita karfinta a siyasance a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 62 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Nuwamba-1953M. Dr Jonas Salk wani likita dan kasar Amurka ya gano kwayar cuta wacce take haddasa cutar shan inna. Cutar shan inna dai tafi shafar yara kanana ne yan kasa da shekaru biyar.

Bayan gano kwayar cutar da kadan ne Dr Jona Salk ya kuma samar da allurar riga kafin cutar. Aikin Dr Salk dai ta shiratarda rayukan mutane da dama a duniya. Inda a halin yanzu dai an kawo karshen cutar a kasashen duniya da dama, duk da cewa har yanzun akwai wasu kasashen kadan da basu rabu da cutar ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Nuwamban-1982M. Shahid Ahmad Asir wani musulmi dan kasar Lebanon ya yi sa’a ya tarwatsa cibiyar rundunar sojojin HKI da ke garin Soor na kasar ta Lebanon, inda a harin neman shahada wanda Ahmad Asir ya kai kan cibiyar yayi sanadiyyar halakar sojojin yahodawa 89 da kuma raunata wasu 86. Kafin haka dai sojojin HKI sun mamaye kasar Lebanon da kudancin kasar har zuwa birnin Beyrut babban birnin kasar. A lokacin mamayar dai sojojin yahudawan sun kashe dubban al-ummar kasar Lebanon da kuma Palasdinawa a sansanoninsu da ke Sabra da Shatila a cikin watan Satumba na wancan shekara. Sai dai bayan halakar sojojin su a Soor, a dole yahudawan suka janye sauran sojojinsu zuwa kan iyakar kasashen biyu.

=================================================================

Yau Alhamis 21-Abaan-1394H.SH=29-Muharram-1437H.K.=12-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Abaan-1293H.SH. Malaman shi’a a kasar Iraqi sun bada fatawar jihadi kan turawan Ingila yan mulkin mallaka wadanda suke kokarin mamayar daular Usmania.

A lokacin dai kasar Iraqi wani bangare ne na daular Usmania. Duk tare da zaluncin da sarakunan daular Usmaniyya suke masu, malaman shi’a sun bukaci mabiyansu da kare daular daga fadawa hannun turawan Ingila yan mulkin mallaka. Sai dai maimakon sarakunan Daular Usmaniyya su yi yaba da hakan sai suka dira a kan yan shi’ar Iraqi suka mukucesu. Sai dai hakan ya bawa turawan dama suka mamaye kasar Iraqi a lokacin suka kuma tarwatsa daular Usmania daga baya. Sai dai bayan tarwatsewar daular Usmania malaman malaman shi’an a Iraqi sun sake kiran jihadi don korar turawan daga kasar Iraqi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 77 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Muharram-1360H.K. Aya. Sayyeed Ali Hujjat Kooh-Kamre’ee daya daga cikin manya manyan malaman addini a yankin Azarbajan na arewa maso yammacin kasar Iran ya rasu. Aya. Kooh-Kamre’ee ya kammala karatunsa na shahar fage a mahaifarsa Tabriz daga nan ya je birnin Najaf mai tsarki na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin ya kuma sami darajar injtihadi.

A lokacinda Aya. Hujjat zai dawo gida Iran malamai da dama ne bi shi suka dawo tare da shi . A gida ma malamai da dama suka dawo makarantarsa inda ya zama makoma ko marja’I garesu da kuma mutanen yankin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Nuwamba-1956M. Sojojin HKI sun sake aikata wani kisan kiyashi ga Palasdinawa mazauna garin Rafa na yankin zirin Gaza wanda suke mamaye da shia a lokacin. A wannan karon dai yahudawan sun aiwatar da kisan kiyashin kwana gudu bayan an shelanta tsagaita bude wuta tsakaninta da kasashen Ingila da faransa a bangare guda da kuma kasar Masar a dayan bangaren, a yakin da ake kira yakin mashigar ruwa ta Swiz.

Palasdinawa 110 ne yahudawan suka kashe sannan wasu fiye da dubu guda suka ji rauni.

================================================================

Yau Jumma’a 22-Abaan-1394H.SH=01-Safar-1437H.K.=13-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1400 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Safar-37H.K. An fara marhala ta karshe na yankin da Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (a) ya shiga da Mu’awiya dan abi Sufyan a wani wuri da ake kira siffin a cikin kasar Iraqi.

Bayan mutuwar khalifa na ukku, da kuma bai’ar da sahabbai suka yi wa Imam Ali(a) Mu’awiya dan abi sufyan wanda ya kasance walin yankin shama tun lokacin khalifa na biyu ya ki ya masa bai’a. Banda haka ma Mu’awiya ya fage da neman jinin khalifa Usman ya shiga yaki da Imam Ali (a). Amma a marhala ta karshe a yakin mayakan Imam Ali(a) sun kusan kama Mu’awiya a hannu, amma sai Mu’awiyan ya cewa mayakansa su daga alkur’anai kan masuna da sunan dakatar da yaki da kuma sulhuntawa. Imam Ali (a) ya fadawa mayakansa kan cewa hakan yaudara ne amma wasu daga cikinsu wadanda daga baya ake kiransu khawarijawa sun yaudaru da hakan, suka kuma tilastawa Imam Ali(a) dakatar da yakin, suka kuma tilasta masa karban taron sulhuntawa na daumata jandal.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Safar-61H.K. Ayarin iyalan gidan Imam Husain(a) wadanda suka zama ribatattun yaki a hannun sojojin Yazidu dan mu’awiya bayan yakin Karbala ta isa kasar Sham. A zaman da suka yi a kasar Sham dai ayarin karkashin jagorancin Imam Aliyu zainul-Abideen (a) da ammarsa Zainab (s) sun isar da sakon yakin karbala ga mutanen sham kamar yadada ya dashe. Musamman a jawaban da suka gabatar a fadar yazid dan mu’awiya. Yazid tsorata da yadda wadannan shuwagabanin ayarin suka bayyana asiransu suka kuma kunyatasu a gaban mutanensu Hakan ya sanya yazid ya dorawa walinsa na Kufa Ubaidullah bin ziyad laifin kashe imam Husain(a). Sannan hakan ya tsoratarshi ya sallame su suka koma madina.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Abaan-1375H.SH. Aya. Sayyeed Murtada Pasandide yayan Imam Khomaini(q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya rasu. Aya. Pasandini ne ya dauki nauyin renon kaninsa Imam khomaini (q) bayan shahadar mahaifinsu Aya. Mustafa. Pasandide ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malaman zamaninsa a birnin Esfahan. Daga nan ya dawo gida Khomain inda ya ci gaba da karantarwa. Aya. Pasandine ya sha gurfana a gaban kotun soje na sarakunan Palawi kan saba masu dangane da hana mata sanya hijabi a Iran da kuma goyon bayan da yake bawa yunkurin kaninsa Imam Khomaini(q) na kawo sauyi a kasar Iran.

Imam Khomani (q) yana matukar girmama yayan nasa wanda ya kula da shi tun bayan sun rasa mahaifinsu.

==================================================.

Yau Asabar 23-Abaan-1394H.SH=02-Safar-1437H.K.=14-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1316 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Safar-121H.K. Zaid bin Aliyu bin Husai dan limami na hudu daga cikin iyalan gidan manzon All..(s) ya yi shahada. Zaidu ya tashi ne don daukar fansar jinin kakansa Imam Husain (a) wanda sarakunan bani umayya suka zubar a kasar Karbala a shekara ta 61 H.K. Yakin da zaidu da magoya mabansa suka yi da sarakunan bani umayya dai ya sake kunna zafin da musulmi suka ji na kashe Imam Husai a kasar Karbaka, kuma fakinsa, an sami irin wadan nan yankure yunkuren wadanda suka hada da na Tawwabin da kuma mukhtar athakafi. An kashe zaidi ne a garin Kufa sannan aka rataya gawarsa a kasuwa na wasu shekaru wai don tsoratar da duk wanda yake son fada da sarakunan bani umayya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 126 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Nuwamba-1889M. Aka haifi Jawaharlal Nehru tsohon Priministan kasar India kuma daya daga cikin fitattun shuwagabannin kasar wadanda suka samarwa kasar Enci daga hannun turawan ingila yan mulkin mallaka. An haifi Nehru a garin Al..abad a shekara 1889M ya kammala karatunsa na jami’a a fannin ilmin sanin shari’a wato Law. Bayan kammala karatun Nehru ya shiga kungiyar gwagwarmaya da turawan ingila yan mulkin mallaka dun kwatarwa kasarsa encin kai. Sau da dama Nehru yana shiga gidan yari don hakan. Bayan samun nasara da kuma encin kan kasar India a cikin watan Augustan shekara 1947M, Nehru ya rike kujerar Priministan kasar na tsawon shekaru 16. Banda haka Nehru ya rubuta littafai wadanda suka hada da “Gano India, Dubi a cikin tarihin duniya da kuma Rayuwata. Nehru yam utu a shekara ta 1964M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 126 da suka gabata a rana irin ta yau wato 126 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Nuwamba-1889M. Aka haifi Taha Husain, wani marubuci kuma masanin adabin larabci a kasar Masar. Husain ya rasa idanunsa tun yana karami amma wannan bai hana shi ci gaba da karatu ba, har ya sami darajar doktora a jami’an sarbon na kasar Faransa a shekara 1918M. Taha Husain ya tainaka wajen kawo ci gaban ilmi a kasar Masar inda ya assasa Jami’ioi a Eskandariyya da kuma AsyuD duk a kasar Masar. Sanna ya taba zama ministan al-adu na kasar Masar. Banda haka Taha Husain ya rubuta littafai wadanda suka hada da -. «تاریخ ادبیات عرب» و «کتاب الایام» (آن روزها) Taha Husain ya rasu a shekara 1973M.

=======================

Yau Lahadi 24-Abaan-1394H.SH=03-Safar-1437H.K.=15-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1380 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Safar-57H.K. Aka haifi limami na biya daga cikin Limamai masu tsarki na gidan annabci wati Imam Mohammad Biqir (a) a garin Madina. A cikin shekaru 19 da ya yi yana rike da ragamar jagorancin al-ummar musulmi bayan shahadar mahaifinsa Imam Sajja (a). Imam Mohammadul Bakir ya bunkasa ilmi a cikin al-ummar kakansa, ya kuma yada ilmi a cikin al-ummar. Imam Bakir (a) da dansa Imam Sadiq (a) su ne suka fara kafa Jami’a a Musulunci a birnin Madina. Amma dayan bangaren kuma bai bar gwagwarmaya da azzaluman shuwagabannin bani Ummayya ba wadanda suka kashe shi a shekara ta 114H.K. Muna taya al-ummar musulmi a murnan haihuwar Imam Mohammad Al-Bakir (a).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Safar-1369H.K. Babban malami kuma malamin tarbiyya Mirza Mohammad Ali Sha’abadi ya rasu. Mirza Sha’abadi ya fara karatun addini a gaban mahaifinsa wanda shima babban malami ne a zamaninsa. Bayan kammala karatun sharar fage ya je birnin Najaf na samira na kasar Iraqi inda ya yi karatu a gaban maun manyan malamai na lokacin. Bayan dawowarsa gida da farko ya zauna Tehran, sannan daga baya ya koma birnin Qum inda ya ci gaba da karantarwa. Mirza Sha’abadi ya na dalibai da dama daga cikinsu akwai Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran . Imam ya na fada dangane da malaminsa cewa “ A duk tsawon rayuwata ban taba ganin mai tausayi irin Aya. Sha’abadi ba”.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Nuwamba-1988M. Aka shelanta kafa entacciyar kasar Palasdinu a wani zama wanda majalisar shoora ta Palasdinawa ta gudanar a kasar Algeria. Banda haka sanarwan ta bayyana cewa baitul muqaddasi shi ne babban birnin kasar ta Palasdinu. A cikin kwanaki 10 kasar kasashe 54 a duniya suka amince da sanarwan na Algeria suka kuma yarda da cewa Yasar Arafat ne shugaban kasar ta Palasdinu. Sai dai a dayan bangaren kuma kudurorin majalisar dinkin duniya na 181 da kuma na 242 duk sun amince da samuwar HKI a kan kasar Palasdinu. Duk da cewa shugaba Yasar Arafat ya bayyana wannan matsayin a taron babban zauren majalisar dinkin duniya a cikin watan yuni na wancan shekara, amma dai gaskiyan lamarin kasar Palasdinu tana karkashin mamayar HKI.

==============================================================

Yau Litinin 25-Abaan-1394H.SH=04-Safar-1437H.K.=16-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 17 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Abaan-1377H.SH. Allamah Mohammad Taqee Jaafari babban malamin falsafa a nan kasar Iran ya rasu. An haifi Allamah Jaafari a shekara ta 1304 H.SH a garin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar Iran. Allamah Jaafari ya haddashe Alqur’ani tun yana karami. Amma talauci ya hana ci ci gaba da karatu na wani lokaci, inda ya shiga aiki yana amfani da ragowar lokacinsa don karatu. Allah Jaafari yana dan shekara 15 ya koma karatu gadan gadan a birnin Qum na kasar Iran. Bayan wani lokaci ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa. Allam Jaafari ya dawo Iran a shekara ta 1336H.SH. inda ya shiga karantawa da rubuce rubuce. Daga cikin littafan da Allahmah Jaafari ya rubuta akwai «ترجمه و تفسیر نهج البلاغه» a cikin mujalladai 27. Sai kuma «جبر و اختیار» da littafi mai suna (( hakkin bil’adama a mahangar Musulunci da kasashen yamma)).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 15 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Abaan-1379H.SH. Hujjatul Islam Mohammad Hadi Amini Najafi babban malamin adini a nan Iran ya rasu. An haifi najafi a shekara ta 1310 H.SH a garin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar Iran. Najafi ya koma kasar Iraqi da zama tare da mahaifinsa Allamah Amini wanda ya rubuta littafin –Algadir- A kasar Iraqi ne ya shiga jami’a ya sami dijiri na farko da na biyu. Bayan haka ya je jami’an al-azhar ta kasar Masar inda ya sami darajar doktora a adabin larabci. Bayan dawowarsa gida Iran Hujjatul Islami Najafi ya ci gaba da karantarwa a Jami’an Tehran yana kuma rubuce rubuce . daga cikinsu akwai «معجم رجال الفکر و الادب» da kuma «اعلام نهج البلاغه» .

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Abaan-1359H.SH. Mayakan sa kai da sojojin kasar Iran sun sami nasara hana sojojin mamaya na kasar Iraqi shiga garin Susangar da ke kan iyaka da kasashen biyu. Shaheed Dr Mustafa Chamran ministan tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lokacin ne ya jagorancin mayakansa wadanda basu fi 200 suka fuskanci tankunan yaki da makaman ikgwa na sojojin sadam Husain na tsawon kwanaki ukku ba tare da ci ko sha ba. Daga karshen sun sami nasara korar sojojin mamaya daga kasar.

==============================================================.

Yau Talata 26-Abaan-1394H.SH=05-Safar-1437H.K.=17-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Safar-61H.K. Sayyida Ruqayya diyar Imam Husain (a) ta yi shahada a fadar yazid dan mu’awiya. Mahaifiyar Ruqayya ko Fatima diyar Imam Husain ita ce Umma Ishaq diyar Talha.

Ruqayya ta zo Karbala tare da mahaifinta Imam Husain (a) wanda yake tsananin sonta kamar yadda take sonshi. Bayan shahadar mahaifinsa tana daga cikin wadanda sojojin yazid suka kama suka yi ta yawo dasu daga Kufa zuwa Sham. A lokacinda Rukayya yar shekaru 5-6 ta ga kan Mahaifinta a cikin wani akwati a Fadar yazid sai ta jefa kanta a kan kan ta rasu. A halin yanzu kabarinta ya zama abin ziyara ga masoya iyalan gidan manzon All…(s). a birnin Damascus na kasar Syria.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 146 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Nuwamba-1869M. Aka bude mashigar ruwa ta Swiz wacce ta hada tekun medeterenian da kuma Tekun Malia. Wani injinia dan kasar Faransa mai suna Ferdinand de Lesseps ya gani mashigar a cikin shekaru goma. Mashigar tana da tsawon kilomita 168 da kuma Fadi tsakanin mita 120-200. Don muhiammancin wannan mashigar turawa yan mulkin mallaka sun yi jayayya a tsakaninsu don samun iko da ita. Amma a shekara ta 1956M gwamnatin kasar Masar ta maida mashigar karkashin ikonta wanda ya janyo mata yaki da kasashen Britania Faransad da kuma HKI. Mashigar dai ta takaita zirga zirgan jiragen ruwa tsakanin Turai da Asia sosai, idan an kwatanta da zagayawa da jiragen ruwa suke yi ta Afrika ta kudu zuwa da dawowa daga Turai.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Nuwamba-1982M. Aka kafa “Majalisar juyin juya halin kasar Iraqi” a nan kasar Iran. Majalisar gamayyar kungiyoyi masu adawa da shugabancin Sadam Husain na kasar Iraqi ne. A lokacinda aka kafa majalisar dai kasar Iran tana cikin yaki da Sadam Husain. Don haka dakarun Majalisar sun shiga yaki tare da Iraniyawa don ganin bayan gwamnatin Sadam. Bayan dakatar da yaki da kuma mamayar da Sojojin Amurka da Britania suka yiwa kasar Iraqi a ashekara 2003M. Majalisar ta kaura zuwa cikin kasar Iraqi inda ta ci gaba da damawa cikin harkokin siyasa na kasar. Aya. Bakir Hakim shi ne shugaban majalisar na farko, ya kuma yi shahada a cikin watan Augustan shekara ta 2003 jim kadan bayan komawarsa kasar ta Iraqi. Sannan majalisar ta chanza sunansa daga baya don dacewa da ayyukan da take yi a kasar.

======================================================.

Yau Laraba 27-Abaan-1394H.SH=06-Safar-1437H.K.=18-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 176 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Nuwamba-1839M. Mutanen kasar Algeria sun fara marhala na biyu na yaki da turawan Faransa yan mulkin mallaka wadanda suke mamaye da kasarsu 1830M. karkashin jagorancin Abdulkadir bin Muhyiddeen . Amir Abdulkadir ya fara yakar turawan da sojoji dubu 50 daga shekara 1839-1847M. Sai dai faga karshe Turawan sun kama shi a shekara 1947 suka jefa shi a kurkuku. Sanna bayan karni guda da mamayar kasar ta Algeria wani borin ya sake tashi inda daga kasarshe kasar ta sami encin kai a shekara 1962M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 112 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Nuwamba-1903M. Aka kulla yerjejeniyar mashigar ruwa ta Panama tsakanin gwamnatin kasar ta Panama da gwamnatin Amurka, inda Amurka ta bada kudu dalar Amurka miliyon goma sannan tana biyar dala dubu 250 a ko wace shekara har illamasha All.. Amma daga baya mutanen kasar sun ki amince da hakan a shekara 1978M inda shugaba Jimy Carter na kasar Amurka da kuma tokoransa na kasar Panama suka sake kulla wata yerjejeniyar wacce ta bukaci Amurka ta mayarwa kasar Panama Mashigar a shekara 1999M. Mashigar Panama tana da tsawon kilomita 68, kuma ita ce ta hade Tekun Atlantic da tekun Pecific daga yammacin nahiyar Amurka.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Abaan-1358M. Bayan makonni biyu da kwace ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tehran wanda daliban Jami’a suka yi da kuma kama ma’aikatan ofishin kimani 50 a matsayin yan leken asirin Amurka a cikin kasarsu. Imam Khumaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bukaci daliban su sallami mata da kuma bakaken fata daga cikin Amurkawa da suke garkuwa da su. Imam ya bada dalilai na cewa Musulunci yana da hukunci na musamman gamata, da kuma wadanda aka zalunta. Tunda har yanzun ba’a tabatar da laifuffukansu ba ana iya sallamar mata da kuma bakeken fata daga cikinsu. Da haka neaka sallami mutane 13 daga cikin Amurkawan suka koma gida.

====================================================.

Add comment


Security code
Refresh