An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 19 January 2016 17:51

Yahudawan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Keta Hurumin Masallacin Qudus

Yahudawan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Keta Hurumin Masallacin Qudus
Tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida sun kai wani farmakin keta hurumin Masallacin Qudus karkashin kariyar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a yau Talata.

Gidan talabijin na Al-Aksa ya watsa rahoton cewa; Wasu gungun tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida da suke samun kariyar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kutsa cikin Masallacin Qudus a yau Talata ta hanyar mashigar Babul-Magharibah, sannan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da suke rufa musu baya suka tsare hanyoyin shiga Masallacin domin hana Palasdinawa shiga Masallacin domin gudanar da sallah.

A gefe guda kuma Sheikh Salah Akramawi limamin Masallacin na Qudus ya koka kan yadda yahudawan sahayoniyya suke ci gaba tone karkashin Masallacin Qudus da sunan gudanar da ayyukan ibadu da kuma janyo masu yawon bude ido lamarin da a karshe zai yi sanadiyyar rusa Masallacin kamar yadda suke son ganin haka.

Add comment


Security code
Refresh