An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 18 January 2016 16:25

Ko kunsan 1-30 Mehr 1394 Hijira Shamsiyya

Ko kunsan 1-30 Mehr 1394 Hijira Shamsiyya
Yau Laraba 01-Mehr -1394H.SH=09-Zulhajji-1436H.K.=23-Satumba-2015M.

Yau Laraba 01-Mehr -1394H.SH=09-Zulhajji-1436H.K.=23-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau ce ranar Arafa 9 ga watan Zulhajji, ranar da Al.. ya umurci bayinsa masu hajji su tsaya a kusa da dutsen arafa su yi addu’oi don neman rahamarsa. Ga wadanda basu je hajji ba suma su yawaita addu’o’I . Akwai ayyuka ibada masu yawa wadanda ake gudanarwa a cikin irin wannan ranar. Daga cikinsu akwai addu’ar Imam Husain (a) na ranar arafa.

Har’ila yau a iran wannan rana ce shekara 1376 da suka gabata wato 9-Zulhajji-60H.K. Muslimu bin Akil dan ammin Imam Husain (a) kuma jakadansa zuwa mutanen Kufa ya yi shahada. Da farko mutanen Kufa sun karbeshi sun kuma yiwa Imam Husain Mubaya’a , bayan da Abaidullah bin Ziyar ya zama walin Kufa, ya tsoratar da su, sun dawo daka rakiyar Imam Husain (a) sun kyale Musulimu bin Akil shi kadai har ya shiga hannun ma’aikatan Abaidullah bin Zoyad wanda ya sa aka jefoshi daga samun fadarsa ya fadi a kasa yay i shahada a rana irinn ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 113 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Mehr-1281H.SH. Aka haifi Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a garin Khomain wanda ke tsakiyar kasar Iran. Yayi karatu a gaban manya manyan malamai wadanda suka hada da Aya. Abdulkarim Ha’iri, Aya. Burujadi da Aya. Shaabadi. Har’ila shima ya tarbiyantar da dalibai masu yawa wadanda suka kasashen tare da shi a yunkurinsa na kafa Jamhuriyar Musulunci a Iran. Imam ya kalubalanci gwamnatin sarki Sha kan abubuwa da dama daga cikinsu akwai rigar kariyar da sarkin ya bawa Amurkawa ma zauna Iran kan duk laifinda suka aikata, wanda ake kira kapitalasion. Kan wannan batun ne aka tilasta masa gudun hijira zuwa kasashen turkiyya, Iraqi da kuma Faransa na tsawon shekaru kimani 15. Imam ya dawo Iran a cikin watan Febrerun -1979 ya kafa Jumhuriyar musuluni, ya kuma kula da ita na tsawon shekaru 10. Shekaru 8 daga cikinsu ya shiga yaki da kasar Iraqi. Daga karshe ya rasu a cikin watan yulin shekara 1988m yanadan shekara 88 a duniya, a halin yanzun Hubarensa na kusa da makabartan Beheshti Zahra a nan Tehran inda dubban dubatan masoyansa suke ziyartarsa a ko wace shekara.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 83 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Satumban-1932M. Aka kafa kasar saudia kuma Abdulaziz bin Saud ya zama sarkin kasar. Kafin haka dai kasar Hijar, kasar manzon Al…(s) tana karkashin daular Musulunci ta Usmania ce, amma bayan yakin duniya na biyu turawa sun tarwatsa daular yankunanta daban daban suka balle daga cikin yankin Hajas wace sharifi Makka yake jagoranta ta balle sai sai dangin Ali saud tare da taimakon turawa sun kwace yankin hajas daga hannnun sharifu Makka suka kuma kafa kasar saudia a rana Iran ta yau. Kasaudia dai ta shahara wajen dangantakarta da kasashen turai da Amurka.

==============================================

Yau Alhamis 02-Mehr-1394H.SH=10-Zulhajji-1436H.K.=24-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 10-Zulhajji –na wannan shekara ta 1436H.K. wato ranar idin layya. A rana irin ta yau ce mahajjata suke aiwatar da ayyukan hajjia masu muhimmanci wadanda suka hada da jifan shaidan layya aski da kuma dawafin dakin Kaaba. Musulmi suna koikoyo ne da Annabi Ibrahim (a) wanda All..Ta’ala ya umurce shi ya yanka dansa Isma’il, amma bayan da shi da dansa suka mika kai sai Al..ya fansheshi da rago. Wannan yana nuna mika kai ga umurnin Al..da kuma rinjayar son zuciya . Muna taya al-ummar musulmi munar sallah babba da fatan Al…ya maimaita mana.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 372 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Satumba-1643M. Yankin Scortland a kasar Britania ta hadewa yankin Ingila suka zama kasa guda. Yankin Scortland dai tana arewacin kasar Britania, tana samun ruwan sama mai yawa, da dazuzzuka masu ciyayi da koguna. Bangarorin biyu sun sha shiga yaki a tsakaninsu. Amma a shekara ta 1643M suka kawo karshen yake yake a tsakaninsu suka kuma dunkule suka zama kasa guda.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Mehr-1357H.SH. Jami’an tsaro na kasar Iraqi sun yi kawanya ga gidan Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Najaf na kasar Iraqi. Gwamnatin kasar Iraqi ta lokacin ta bukaci Imam ya dai jawabai masu ingiza mutanen kasar Iran su yi bori wa sarkin kasar ta kafafa yada labarai da kuma jawaban da yake yadawa da cassette cassette. Imam Khomani (q) ya ki amincewa da bukatar gwamnatin ta Iraqi ya ce duk inda yake a duniya zai ci gaba da yin abinda ya zama wajibi a kansa. Daga gwamnatin ta bukace shi da ya bar kasar. Wannan shi ne yay i sanadiyyar hijirar Imam (q) zuwa kasar faransa inda ya ci gaba da jawabansa har zuwa lokacinda ya kuduri anniyar dawowa Iran, ya dawo ya kuma kifar da gwamnatin sarkin ya kuma kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara 1979M.

===========================================================.

Yau Jumma’a 03-Mehr-1394H.Sh=11-Zulkida-1436H.K.=25-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 81 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Mehr-1313H.SH. Aya. Mirza Abulkasim Kabir Qumi babban malamin addini a nan Iran ya rasu. An haifi Aya. Qummi a shekara ta 1262H.SH. bayan ya kammala karatunsa na sharar fage a garin Qum ya kammala karatu a gaban manya manyan malamai wadanda suka hada da Mirza Khalil Tehrani Najafi, Okhunde Khurasani da sayyeed Kazim Yaddi dukkaninsu a birnin Najaf na kasar Iraqi. Sai kuma dalibansa sun hada da Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran , Aya. Galpeyagani, Okhunde Mulla Hamedani da wasu da dama. Bayan shekaru 73 masu albarka Aya. Mirza Qymi ya rasu a ranar 03-Mehr-1313 a birn Qum.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 46 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Satumba-1969M. Aka kafa kungiyar kasashen musulmi ta OIC. Bayan majalisar dinkin duniya dai kungiyar OIC ce kungiyar kasashe mafi girma a duniya. Inda take da kasashe membobi 57 a cikin nahiyoyi 4 a duniya.

Dalilan kafa wannan kungiyar sun hada da samun hadin kan kasashen musulmi don fuskantar ta’asan da HKI take aikatawa a kasar Palasdinu. An kafa kungiyar ne bayan wata gobarar da HKI ta haddasa a cikin masallacin Qudus a lokacin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Satumba-2003M. Prof: Edwad Sa’eed wani malamin adabi ba Palasdine ya rasu. An haife shi a shekara ta 1935M. Yana dan shekara 17 a duniya ya sami damar tafiya zuwa Amurka don karin karatu a jami’ar Hawad. Abinda ya sa sa’eed ya shahara shi ne rubutunsa da kuma maganganunsa kan zaluncin da akewa al-ummar Palasdinu a kasarsu.

Edwad Sa’eed ya rybuta littafai da dama daga cikinsu akwai. –Al’adu da mulkin danniya- Siyasar kwacen mallaka- da kuma –aikin jarida a Musulunci.

A shekara ta 1977M ya shiga majalisar Palasdinawa sannan ya fice daga majalisar a shekara ta 1991 bayan sulhun da shuwagabannin Palasdinawan suka shiga HKI .

==========================================================.

Yau Asabar 04-Mehr-1394H.Sh=12-Zulkida-1436H.K.=26-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 496 da suka gabata a rana irin ta yau wato Allama Aliyu bin Husain Karaki, wanda aka fi saninsa da muhakkin karaki daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu. An haifi muhakkik karaka a yankin Jabal Amil na kasar Lebanon, kuma ya fara karatu a gida kafin ya ji sauran kasashen musulmi don kammala karatu. Bayan haka ya dawo kasar Iran da zama inda ya bude cibiyoyin ilmi da dama yana kula da su yana kuma rubuce rubuce.

Muhakkin karaka ya shahara da sanin ilmin tarihi a zamaninsa musamman a cikin littafinsa mai suna «جامع المقاصد»، har ila yau yana da wasu littafan wadanda suka hada da «شرح شرایع» و «رساله عدالت».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 32 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Zulhajji-1404M. Aya. Mirza Muhammad Bakir Oshtiyani daya daga cikin manya manyan malamai a nan Iran ya rasu. Hajj Mirza Mohammad Bakir Oshtiyani da ne ga Mirza Ahmad sannan jika ga Mirza Mohammad Hassan Oshtiyoni wadanda suka kasance jagorori ko shuwagabannin yunkurin haramta taba a nan Iran a shekara ta 1323H.SH. don karya wani kamfanin kasar Britania wanda sarkin Iran na lokacin ya kebance shi da shigo da shi kasar.

Bayan karatun sharar fage a nan Tehran Mirza Oshtiyani ya kama hanyar Najaf na kasar Iraqi inda yay i karatu a gaban manya manyan malamai wadanda suka hada da Aya. Diya’udeen Iraqi, Sayyeed Abul Hassan Esfahani da kuma mirza Na’eeni. Bayan kammala karatu ya dawo nan Tehran inda ya ci gaba da karantarwa har zuwa rasuwarsa yana dan shekara 81 a duniya. Kabarinsa na garin Rai a nan kusa da birnin Tehran.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 3 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Satumba-2012M. Wasu yan ta’adda masu adawa da gwamnatin kasar Syria sun harbe yan jarida masu aiki wa tashoshin television na Presstv da kuma Al-Alam a birnin Damascus na kasar Syria. Moyo Nasir kirista ne dan kasar ta Syria an haife shi a ranar 30-Yuli-1979M, ya kammala karatun jami’a a jami’ar Coplon da ke birnin Newyork kasar Amurka, tun lokacinda aka fara yaki a kasar Syria ya fara aikewa Presstv rahotanni. Sai kuma Husain Murtada shugaban ofishin Al-Alam a birnin Damascus na kasar Syria. Nasir yay i shahada a yayinda Murtada ya warke daga harbin da yan ta’addan suka yi masa a kafa.

=========================================================.

Yau Lahadi 05-Mehr-1394H.Sh=13-Zulkida-1436H.K.=27-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 98 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Zulhajji-1338H.K. Aya. Mirza Mohammad Taqi Ha’iri Shirazi ya rasu. Aya. Shirazi yana daga cikin fitattun malaman Imamiyya a lokacin sannan dalibi ne ga Aya. Shirazi na farko. Ya rayu a lokacinda turawan ingila suka mamaye kasar Iraqi a shekara 1920M. Aya. Shirazi ya shahara da fatawarsa na yin jihadi kan taruwa yan mulkin mallaka. Fatawar tasa ta yi tasiri so sai wajen janyewar turawan daga kasar Irai a lokacin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 75 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Satumban-1940M. Kasashen da suke yi kawance da kasar Jamus a yakin duniya na biyu sun rattaba hannu a kan wata yerjejenia ta aiki tare a garin Poolodeen na kasar Jamus. Wannad yerjejeniyar ce ta hada kan kasashe ukku Jamus, Italia da kuma Japan a bangare guda a yakin duniya na biyu. Bayan wannan yerjejeniyar ne kasar Japan ta fadawa Amurka da yaki wanda ya shigo da ita cikin yakin a bangaren kawancen kasashen Britania Faransa da tarayyar Soviet. An kawo bayan yakin ne bayan da Amurka ta jefa makaman nuklia kan kasar Japan a cikin watan Augustan shekarata 1945.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Mehr-1360H.SH. Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sami nasara mai girma ta farko a lokacinda suka kawo karshen killacewar da sojojin kasar Iraqi suka yiwa birnin Abadan a kudu maso yammacin kasar Iran. Sojojin Sahan Husain sun yi wa garin Abadan mai matatar man Fetur mafi girma a kasar kawanya na tsawon shekara guda sun kuma zuba sojoji da kayakin yaki don kada garin ya kubuce masu. Amma Imam Khomain (q) ya bukaci sojojin Iran sun kawo karshen wannan killacewar da sauri. Don haka a wani farmaki wanda ake kira “Thaminul-a’imma” a rana irin ta yau sojojin Iran suka dawo da ikon gwamnatin Jamhuriyar Musulunci a garin na Abadan.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Satumba-1996M. Kungiyar Taliban ta masu kishin musuluni a kasar Afganistan ta kwace iko da birnin Kabul babban birnin kasar. An kafa kungiyar Taliban ne a shekara ta 1994M a kasar Pakistan tare da tallafin kasashen Amurka da kuma Saudia. Taliban ta fara mamayar kudanci da kuma yammacin kasar Afganistan ne kafin su kai ga kwace Kabul. Kafin su shiga birnin da kwana guda ne sojojin kasar ta Afganistan karkashin Ahmad Sha Mas’ud suka janye daga birni.

A cikin shekaru kimani 4 wanda Taliban ta yi iko da kasar Afaganistan ta nuna tsauri wajen mu’amala da musulman kasar da sunan addini, musamman mata. Inda suka haramta masu karatu. Wannan ya sa mutanen kasar suka ki su, sannan daga karshen a shekara ta 2001 kasar Amurka tare da kawayenta suka kauda Taliban daga ikon kasar ta Afganistan.

=======================================================.

Yau Litinin 06-Mehr-1394H.SH=14-Zulhajji-1436H.K=28-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 45 da suka gabata a ran irin ta yau 28-Satumba-1970M. Jamal Abdunnasir shugaban kasar Masar ya rasu. An haifi Abdunnasir a shekara 1916M. Abdunnasair ya shiga yakin Larabawa da HKI a shekara ta 1946M sannan yana daga cikin sojojin da suka yiwa Sarki Faruk juyin mulki a shekara 1952M. Sai kuma shekaru biyu bayan haka ya zama shugaban kasa. Sai kuma a shekara 1956M Jamal Abdunnasir ya maida mashigar ruwa da Swiz ta zana ta kasa. Wanda hakan ya jawo masa yaki da kashashen Ingila, Faransa da kuma HKI, amma Masar ce ta sami nasara a karshen yakin. Sai kuma a shekara ta 1958 ya hade kasashen Syria Masar da kuma Yemen suka zama kasa guda, duk da cewa hakan bai doreba sai na tsawon shekaru 3 kacal. Sai kuma a shekara ta 1967 ya shiga yaki da HKI karo na biyu amma suka sha kaye daga karshe Abdunnasir ya rasu a rana irin ta yau a shekara 1970M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Satumba-1996M. Majalisar dinkin duniya ta fitar da wani kuduri wanda ya hana HKI ci gaba da tona hanyar karkashin kasa a kasa da masallacin Al-Aksa a kasar Palasdinu. HKI ta fara gina wannan hanya ce a ranar 23-Satumban-1996M wanda ya jawo rigima da Palasdinawa wanda kuma ya kai da shahadar Palasdinawa da dama. Tun lokacin da HKI ta kwace birnin Qudus a shekara 1967M taka tune tune a gewayen masallacin da niyyar rusa shi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 15 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Satumba-2000M. Al-ummar Palasdinu sun fara wani bori wanda ake kira Intifada a yakunansu wanda HKI take mamaye da su. Palasdinawan sun soma wannan borin ne bayan da Ariel Sharon shugaban Jam’iyyar Lekud na HKI ya shi masallacin Al-Aqsa ya kuma keta huruminsa. Sharon ya shahara da kekashewar zuciya da kuma kisan Palasdinawa kimani 3300 a sansanoninsu da ke sabra da shitila a kasar Lebanon a shekara 1982m. HKI ta yi amfani da tankunan yaki helkoptocin yaki da harbin bindiga don kwantar da borin, inda Palasdinawa da dama suka yi shahada.

===============================================================.

Yau Talata 07-Mehr-1394H.SH=15-Zulhajji-1436H.K=29-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1222 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Zulhajji-214H.K. Aka haifi Imam Aliyu bin Muhammad (a) limami na 10 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) a Madina. Imam Naqiy (a) ya gaji mahaifinsa Imam Al-jawad wajen jagorantar al-ummar musulmi bayan shahadarsa. Imam Hadi (a) ya rayu a lokacinda sarakunan Abbasiyawa suke tsananin rigima a tsakaninsa kan karban madafun iko. A dai dai lokacin ne sarki Mutawakkil Abbasi ya ga cewa Imam Al-hadi (a) hatsari ne da mulkinsa don haka ya tilasta masa yin hijira zuwa cibiyar mulkibsa da ke Samira na kasar Iraqi don sanya ido a cikin harkokinsa. Amma duk da haka Imam Al-Hadi (a) ya tarbiyantar da Taliban manya manyan kamar Sayyeed Hassan Abdul-azim alhasani wanda kabarinsa yake garin Rai a nan kusa da birnin Tehran. Muna taya al-uammar musulmi murnar ranar haihuwar Imam al-hadi (a).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Mehrar-1360H.SH. Hujjatul IslamiSayyeed Abdulkarim Hashimi –Najad daya daga cikin fitattun malaman addini a birnin Mashad a nan iran yay i shahada. An haife shi a shekara ta 1312M, kuma yay i karatu a gaban manya manyan malamai kamar su Aya. Burujadi da Imam Khomaini(q). Banda haka Sayyeed Hashimi Najad ya sha dauri a hannun sarakunan Iran kafin samun nasara. Sannan bayan samun nasarar juyin jya halin Musulunci ya ci gaba da wayar da kan mutane har zuwa lokacinda munafukai makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka kashe shi a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Mehr-1360H.SH. Komandojin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran su biyar sun yi shahada a wani hatsarin jirgin sama a kan hanyarsu ta zuwa Tehran bayan fatahin birnin Abadan a lokacin yakin shekaru 8. Brigate commande Fallah, Yusuf Kulodoos, ministan tsaro Sayyeed Musa Namjoo da kuma Brigate commanda Fakhuri duk sun yi shahada a wannan hatsari.

=====================================================

Yau Laraba 08-Mehr-1394H.SH=16-Zulhajji-1436H.K=30-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 8-Mehr ranar tunawa da Maulana Jalaluddeen Muhammad bin Baha’uddeen wanda aka fi saninsa da Maulawi a nan Iran. An haifi Maulawi a shekara ta 604 H.K. a garin Balkh na kasar Afganistan a halin yanzu. Ya tashi a gaban mahaifinsa wanda shi ma babban malami ne. Bayan ya kammala karatu Maulawi ya shiga karantarwa ya kuma hadu da Muhammad Shamsuddeen babban malamin Erfani wanda ya fahintar da shi abubuwa da dama a ilmin erfan. Daga karshe Maulawi ya rasu a shekara ta 672H.K. yana dan shekara 68 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa 30-Satumba ranar da MDD ta ware don tunawa da bebeye a duniya. Manufar ware wannan ranar shi ne fahintar da mutane halin da kurame suke ciki a duniya don kuma kula da al-amuransu. Daya daga cikin hanyoyin taimaka masu shi ne koyin magana ta ishara ko kuma nunawa da hannu.

Banda wannan mutane zasu fahinci nemar da Al..ya yi masu na ji da gani wadanda suke taimakawa wajen suwwake rayuwarsu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 30 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Satumba-1985M. Charles Richter masanin ilmin kimiyyar lissafi dan kasar Amurk ya rasu. Charles Richter ne ya kirkiro ma’aunin girgizan kasa wanda ake kira Richter. Ma’aunin yana da hawa 9 ne, sannan kafin haka mutane suna auna karfin girgizan kasa ne da yawan asarar da ta jawo.

====================================================

Yau Alhamis 09-Mehr-1394H.SH=17-Zulhajji-1436H.K=01-Octoba -2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 55 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Octoba -1960M. Kasar Nigeria ta sami encin kanta daga hannun turawan Britania yan mulkin mallaka. Turawan sun shigo Nigeria daga kudancin kasar a karshen karni na 19 miladiyya. Sai kuma ashekara 1914M suka hade arewa da kudancin kasar suka zama kasa daya. A shekta ta 1954 ta sami kwarkwaryan encin kai, sai daga karshe wato a shekara 1960 ta sami cikekken enci. Nigeria tana da kabilu fiye da 250 sannan tana da fadin kasa kilomita murabbaee dubu 923 tana makobtaka da kasashen Cmaroo, Chadi, Niger da kuma Benin daga yammacin kasar . yawan mutanen kasar ya kai million 170. Har’ila yau tana da arzikin man fetur da ma’adinai.

**Masu sauraro ko kunsan cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Oktoban- 1949M. Kasar China karkashin ikon Mao Tetse Tung ta shelanta kafa tsarin gurguzu a kasar. Kafin haka dai Mao ya sami goyon bayan manomar kasar wadanda suka yi tattaki tare da shi daga kudancin kasar Zuwa babban birnbin kasar inda suka kori sarakunan kasar karkashin jagorancin sarki chiyon Koi Chech. Sarkin ya dai ya arce zuwa tsibirin Taiwan wanda shi ma yankin kasar China ce amma ya balleta daga kasar. Kafin ranar 1-Octoban -1949 Mao ya karbi iko da dukkanin yankunan kasar China in banda Taiwan,.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru daya ga watan Octoba ranar da aka ware don tunawa da tsoffi. Tsofa wata marhala ce a rayuwa wanda rauni yake bayyana a mutum bayan karfi da yawan kai kawo na kurucciya da zama matashi. Kyautatuwan harkar lafiya da tsabta a duniya yana kara yawan shekarun mutane a duniya, musamman a cikin karni na 19 miladiyya a lokacinda aka kyautata hanyoyin kiwon lafiya da kuma abinci.

Anan Iran dai gwamnati tana kashe kudade masu yawa don kula da lafiya da kuma jin daden tsoffi musamman wadanda suka yi khidima ga kasa. Kuma akan gudanar da bukukuwan na musamman don tunawa da wannan ranar.

===============================================

Yau Jumma’a 10-Mehr-1394H.SH=18-Zulhajji-1436H.K=02-Octoba -2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1426 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Zulhajji-10H.K. Manzon Al..(s) tare da umurnin Al..ta’ala ya bayyanawa musulmi cewa Aliyu dan Abi Talib ne magajinsa bayan rasuwarsa. Manzon Al.. ya bayya haka ne a wani wuri tsakanin Makka da Madina, inda ya daga hannun Aliyu sama a gaban sahabban yana cewa, duk wanda na kasance shugabansa to Aliyu shugabansa ne, Ya ubangiji ka jibanci wanda ya jibanceshi yay i adawa da wanda yay i adawa da shi..” Daga nan aya ta suratl Ma’ida ta sauka tana cewa” A yau ne na cika maku addinininku, sannan kuma na kammala ni’imata a gareku. Don haka wannan rana id ice ga musulmumi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1401 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Zulhajji-35H.K. Imam Aliyu Dan Abitalib (a) ya mince ya karbi khalifancin musulmi bayan yaki amince da hakan na yan kwanaki bayan kashewar Khalifa na ukku. Kafin haka dai bayan kashewar Khalifa na ukku mutane sun yi tururuwa zuwa gidansa don ya karbi bai’arsu. Imam (a) ya shimfida sharudda daga cikinsu zai yi hukunci da alqur’ani da sunnar manzon All..(s) wajen limancinsa. Sai dai bayan ya karbi iko wadanda abin bai yi masu ba sun haddada masa yakoki har guda ukku, wato Jaml, Siffin da kuma Nihrawan. A cikin shekaru 4 da wata 9 da yayi, Imam Ali (s) yay i kokarin dawo da adalci da daidaito tsakakin al-umma.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 764 da suka gabataa rana irin ta yau wato 18-Zulhajji-672H.K.

Khoja Nasirudden Toosi saya daga cikin manya manyan malamai ya rasu. Bayan da mungolawa sun karbi iko da birnin Bagdaza babban birnin daular abbasiyawa a lokacin. Amma bayan karbansu da ikon kasar, sai ya amintar da Khoja Nasiruddeen da mutanensa. Inda yay i afanin da wannan matsayin wajen kare wurare masu muhimmanci ga musulmi wadanda suka hada da lalata wusu karin gidajen ajiyar littafai da kuma cibiyoyin yada ilmi da kuma malamai masu yawa.

Khoja Nasiruddeen Toosi ya rubuta littafai sun kai 80, sannan ya rasu yana dan shekaru 75 a duniya.

===========================================================.

Yau Asabar 11-Mehr-1394H.K.=19-Zulhajji-1436?H.K.=03-Octoba-2015M.

**Masu sauraroro ko kun san cewa shekaru 73 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Octoba-1942M. An cilla kubbo na farko kiran dan adam zuwa sararen samani.

Wani Injiniya dan kasar Jamus mai suna Wirni Brovon yay a kera wannan kobbon, inda ya dora masa makamashi mai nauyin ton 13 mai tsawon mita 14, sannan ya cillaci shi zuwa sama a wani tsibiri a yankin Baltic. Kudun kumbon ya fi tafiyar sauti ya kuma daga zuwa kilomita 180 zuwa sararen samaniya kafin ya sake fadowa kasa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Mehr-1357H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bar kasar Iraqi bayan da gwamnatin kasar ta takaida ayyukansa ta hanashi jawabai da kuma ayyukan yada fahinyarsa ta kafafen yada labarai. Imam ya nufi kasar Kuwai sai dai ita mata ki amincewa da shigarsa kasar don tsaron dangantakarta da sarki sha na kasar Iran. Anan ne Imam ya yanke shawarar komawa kasar Faransa inda ya zauna na yan watanni sannan ya dawo kasar Iran ya kammala jagorantar juyin juyin halin musuluncin kasar zuwa ga nasara.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Octoba-1991M. Kasashen Jamus ta gabas da Jamus ta yamma sun sake hadewa sun zama dunkulalliyar kasar Jamus bayan rabewa na tsawon shekaru 45. A karshen yankin duniya na biyu ne Tarayyar Soviet ta mamaye gabacin kasar Jamus sannan kasashen yamma kuma suka mamaye Jamus ta yamma. A shekara ta 1949M ko wani yanki ya kafa gwamnati mai tsarin tattalin narziki da mulki irin tasu. A shekara ta 1961 Tarayyar Soviet ta gina katanga wacce ta raba kasashen biyu. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara ta 1989 a lokacinda mutane suka kada bongon balin da ta raba kasar biu sannan a rana irin ta yau aka shelanta sake hadawar kasashen biyu.

Yau Lahadi 12-Mehr-1394H.K.=20-Zulhajji-1436?H.K.=04-Octoba-2015M.

**Masu sauraroro ko kun san cewa shekaru 58 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Octoba-1957M. A karon farko a duniya na cilla tauraron dan adama zuwa sararen samadia. Wani masani dan kasar tarayyar Soviet ne yak era tauraron sannan ya cilla shi zuwa sama. A cikin kwanaki 92 da tauraron ta yi a sama ta zagaya duniyarmu hau sau 1400. Tauraron mai suna Sputnik 1 yana da nauyin kilogram 83 da kuma tsawon centimita 85. Tauraron yana da Tranmitoci guda biyu wadanda suke aika da sakonni zuwa duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau 12-Mehr-1357H.K. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi hijira zuwa kasar Faransa bayan da gwamnatin kasar Iraqi ta bukace shi da ya bar kasar. Bayan da gwamnatin kasar Kuwaita ta hana shi shiga kasarta. Imam ya zauna a wani wuri mai suna Nufel Lu Shoto kilomita 50 daga birnin Paris. Imam ya ci gaba da jawabai da kuma aika da sakonni zuwa kasar Iran don nuna mutanensa abinda yakamata su yi. Daga karshe bayan gudun hijira na watannu 4 a kasar Faransa ya koma gida Iran inda ya karasa jagoranci juyin juya halin zuwa ga nasara. Ya kawo karshen tsarin sarauta kasar Iran na shekaru 2500.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Octoba-1982M. Tsohon shugaban kasar Iraqi Ahmed Hassan al-bakari ya mutu yana dan shekara 68 a duniya. Al-bakari ne ya yiwa Abdurrahman Arif juyin mulki a shekara ta 1968m sannan ya ci gaba da mulki da hannun karfe har zuwa shekara 1979 a lokacinda mataimakinsa Sadam Husain ya tilasta masa sauka daga kan kujerar shugabancin kasar a ranar 16-Jenerun-na shekarar.

========================================================.

Yau Litinin 13-Mehr-1394H.SH=21-Zulhajji-1436H.K.=05-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 225 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Zulhajji-1211H.K. Aka kashe AgoMuhammad Khon Qajar, sarkin kasar Iran wanda kuma ya assasa sarautar dangin kajarawa a nan kasar. An haifi Muhammad a garin Gurgun da ke arewacin kasar. Muhammad Khan ya rayu shekaru 16 tare da danginsa a garin Shiraz a tsakiyar kasar, amma bayan da ya ji cewa sarkin Karim Khan bai da lafiya sai ya kama hanyar Mazandaran inda sarkin yake. Sannan tare da tainakon dan uwansa ya sami nasar aka nada shi sarki bayan mutuwar sarki Karin Khan a ranar 11-Jamada-Sani -1200H.K. Muhammad ya ci gaba da mulki har na shekaru 12, inda a ranar idi ta shekara 1212 wasu masu gadinsa suka kasheshi. Bayan kisansa, tunda shi bai haifu ba danuwansa Fat-Ali ya gajeshi a kujerar sarautar kasar Iran.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 107 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Zulhajji-1329H.K. Okhunde Mulla Muhammad Kazim Khurasani daya daga cikin manya manyan malamai a kasar Iraqi ya rasu a birnin Najaf. An haifi Mulla Khurasani a shekara ta 1255 H.K. a garin Mashad na kasar Iran yana dan shekara 12 a duniya ya fara karatun hauza a mashad daga bayan yak aura zuwa Tehran inda yayi karatu a gaban Mullah Hadi Sabziwari, sai a Najaf na kasar Iraqi yay i karatu a gaban Mirza Shirazi, Sheikh Murtada Ansari, Sayyeed Hassan Mudarris. Sannan Okhunde Khurasana ya tarabiyantar da dalibai da dama wadanda suka hada da Mirza Na’ini, Sayyeed Sadruddeen Sadar, Sayyeed Hassan Musarris da sauransa. Okhunde Khurasani ya rubuta litattafai da dama daga cikinsu akwai “کفایةُ الاصول”. Okhunde Khurasani ya rasu a birnin Najafa yana dan shekara 74 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 50 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Mehr-1344H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya isa kasar Iraqi daga gudun hijiran da aka tilasta masa na watannin 11 a kasar Turkiyya. Dalilai da dama suka sa sarki sha ya saka sauya wurin gudun hijirar Imam zuwa Iraqi, daga ciki gwamnatin Turkiyya taki amincewa ya ci gaba da zama a kasarta, sannan suna ganin idan an maida shi Iraqi zai yi shiru don akwai manya manyan malamai wadanda basa tare da ra’ayinsa. Amma Imam ya samarwa kansa hanyar ci gaba da kiransa da kuma gwagwarmaya wanda ya kaiga hukumomin Iraqi suka bukaceshi ya bar kasar bayan gudun hijira na shekary 13, inda ya koma kasar Faransa na dan watannin sannan ya dawo gida a shekara 1357H.SH. Ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

====================================================

Yau Talata 14-Mehr-1394H.SH=22-Zulhajji-1436H.K.=06-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22- zulhajji-60 H.K. Maitham Attammar daya daga cikin sahabban manzon Al..(s) da kuma Amirul muminina (a) ya yi shahada. Maitham ya kasance bawa ne sannan Aliyu (a) ya sayeshi ya kuma enta shi. Amirulmuminina (a) yana sonsa kamar yadda shima yake sonshi. Don haka ne ma ya fada masa yadda azzaluman sarakunan zasu kashehsi don sonsa ga Iyalan gidan manzon All..(s). Maitham ya sha bayyanawa abokansa yadda zai yi shada kamar yadda masoyinsa Imam Ali (a) ya fada masa , amma da lokacin yayi sai Ubaidullah bin Ziyad walin Kufa yana son ya sabawa hakan, amma daga karshe a dole sun kasheshi ta yankan harshensa kamar yadda Imam (a) ya fada.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Mehr-1359H.SH. Gwamnatin kasar Jordan ta bawa kasar Iraqi damar amfani da tashar jiragen ruwa na Aqaba a matsayin tallafi gareta a yakin da ta key i Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sarkin Husain na kasar Jordan a lokacin ya bayyana haka ne ga shugaban kasar Iraqi Sadam Husain a wata ziyara da kwana guda da ya kai kasar Iraqi. Sarki Husain ya bukaci kasashen Larabawa su hada kai don yakar kasar Iran a lokacin. A ranar 31-Shahrivar -1359 H.SH ne kasar Iraqi karkashin shugabancin sadam Husain suka fara mamayar wasu yankuna na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da nufin kawo karshen jaririyan gwamnatin Musulunci da Imam Khomaini (q) ya kafa a kasar. Amma har zuwa karshen yakin sadam Husain bai cimma wannan burin ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato -06-Octoban-1981M. Wani sojojin kasar Masar mai suna Khalid Islam Buli ya bindige shugaban kasar Masar na lokacin Anwar Saadad wanda yake karban fareti a wani biki a birnin alkahira. Khalid tare da abokansa sun kuduri anniyar halaka Anwar Sadat ne bayan da sanya hannu kan yerjejeniyar Comp Devid tare da HKI. Da dama daga cikin musulmi sun dauki hakan a matsayin ha’inci ga musulmi. Don haka ne ma kasashen larabawa da musulmi da dama sun kaura cewa kasar ta Masar. Bayan kisan shugaban, jami’an tsaron kasar sun kama mutani kimani 3000 tare da tuhumarsu da kisan shugaban daga karshe an kashe Khalid da wasu abokansa bayan wata kotun soje ta yanke masu hukuncin kisa.

==========================================================

Yau Laraba 15-Mehr-1394H.SH=23-Zulhajji-1436H.K.=07-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 77 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Zulhajji-1359H.K. Babban malamin ilmin hadisi wanda ya rubuta mafatihil Jinan Abbas Qumi ya rasu a birnin Qum. Abbas qumi yana daga cikin fitattun malaman qarni na 14 hijira kamariya. Ya fara karatuna a Qum sannan ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban Hajj Mirza Husain Noori bayan rasuwar malaminsa ya dawo Qum da zama. Abbas Qumi ya rubu

ta littafai da dama amma wanda aka fi sani daga cikinsu shi ne Mafitihul Jinan wanda ya tattara addu’oee da ziyarori na manzon All…(s) da iyalan gidansa .

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Mehr-1372H.SH. Aya. Husain Muhammadi Laa’eeni daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu. An haifi Aya.Laa’eeni a shekarata 1303H.SH . Bayan kammala karatunsa na sharar fage a nan Iran ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na zamaninsa wadanda suka hada da Aya. Sayyeed Mahmood Shahrudi da Mirza Hashim Amuli. Bayan samun sanarar juyin jaya halin Musulunci a shekara 1357H.SH Aya. Muhammad Laa’eeni ya zama wakilin mutanen mazandaran a majalizar zaben jagora har sau biyu na shekaru hudu hudu. Ya rasuna yana dan shekara 70 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Octoba-2001M. Sojojin kasar Amurka sun fara kai farmaki kan kasar Afganistan da nufin kamo Usama bin Ladan shugaban kungiyar Alka’ida wanda take tuhuma da harin 11-Satumban shekarar, wanda kungiyar Taliban wacce take iko da yankin mai yawa na kasar Afganistan take karewa.

Wannan harin shi ne madomin shiga kasar Afganistan na tsawon shekari fiye da 10 wanda sojojin Amurka da NATO suka yi a kasar suna kashe mutane da sinan kawo karshen Taliban. Amma har bayan ficewar sojojin Amurka saga kasar a bara Taliban tana nan a Afganistan.

==========================================================

Yau Jumma’a 17-Mehr-1394H.SH=25-Zulhajji-1436H.K.=09-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 1428 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Zulhajji-08H.K. Aka saukar da suratuddahar ko insan, bayan da Imam Ali(a) da matarsa Zahrah (s) da kuma yayansu Al-hasan da Al-Husain da kuma kuyangarsu Fidda suka yi azumi na kwanaki ukku a jere, amma kuma suka yi sadaka da abincin buda bakinsu na kwanakin ukku ga miskini, da maraya da fursinan yaki. Al..ta’ala ya yabesu a wannan surar ya kuma yi masu alkawarin ni’imomin aljanna. Wannan surar tana bayyana matsayin da iyalan gidan manzon All…(s) suke da shi a wajen Al..

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Octoban-1962M. Kasar Uganda ta sami encin kanta daga hannun turawan Ingila yan mulkin mallaka. A shekara ta 1890M ne turawan suka mamaye kasar ta Uganda, kuma tun lokacin ne mutanen kasar suka fara gwagwarmayan samun encin kai, kafin shekara ta 1962M, gwagwarmayan ta zafafa wanda ya kai ga turawan suka mika mulki gay an kasar a ranar 09-Octoban- 1962.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 48 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Octoban-1967M. Aka kashe Ernesto Che Guwara wani dan gwagwarmaya da yan mulkin mallaka a yankin Latin Amurka. An haifi Guvara a shekara 1928M a kasar Agentina. Bayan da ya ga irin wahala da talaucin da mutanen yankinsa suke ciki karkashin ikon shuwagabanni masu biyayya ga Amurka Guwara ya shiga gwagwarmaya da irin wadannan shuwagabanni a yankin . Da farko ya hadu da Fudal Castro na kasar Cuba a shekara 1959M. Bayan da Castro ya sami nasara a Cuba sai Guvara ya koma Bolivia inda ya kafa runduna ta kwatar encin kasar . Anan ne hukumar CIA ta Amurka suka gano inda yake suka kama shi da abokan aikinsu sannan aka kashe su a rana irin ta yau.

==========================================================

Yau Asabar 18-Mehr-1394H.SH=26-Zulhajji-1436H.K.=10-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 134 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Octoba-1881M. Kasashe ukku a nahiyar Turai sun yi kawance ta tsaro a tsakaninsu. Kasashen su ne Jamus, Italia da Autria. Kafin haka dai kasashen Jamus da Austria ne suka fara wannan kawancin, sai kuma Italia ta hade da su a ashekara ta 1881M. Manufar wannan kawance ta tsaro dai ita ce, cewa duk wacce aka takala da yaki a cikin kasashe ukkun nan sauran ma zasu shiga yakin a bangarenta. Wannan kawancen dai ana sabonta shi a cikin duk shekaru biyar. A lokacinda aka kulla wannan kawancen dai kasar Italia tana zaman dardar da Faransa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 103 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Octoban-1912M. Aka kafa tsarin jumhuriya a kasar China ko Sin a karon Farko. Sarakunan dangin Manjoo sun fuskanci bori da tawaye na mutanen kasar China har sau 5 a tsakanin shekaru 1907-1911M. Amma da kaka fara na biyar din sarakunan Manjoo sun ga cewa bazasu kai labari ba sai suka bukaci tattaunawa da yan adawa a nan ne aka zauna taburin shawara aka kuma kafa tsarin jumhuriya a ranar 10-Octoban-1912M. aka kawo karshen sarautar dangin Manjoo a kasar .

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Octoban-1949M. Tsibirin Taiwan mai fadin kilomita murabbaee 36 ta shelanta zama kasa da kuma bellewa daga kasar China. Kafin haka dai ya akidar gurguzu masu gwagwarmaya da mulkin shugaba ChiyonkaiChek karka jagorancin Mao sun sami nasara korar gwamnatin kasar suka kafa tsarin gurguzu bayan yakin duniya na biyu. A nan ne shugaba ChiyonkaiChek ya tsere zuwa tsibirin Taiwan, tare da taimakon Amurka ya shelanta bellewar shibirin daga China. Sanna a majalisar dinkin duniya ma, Amurka ta yi amfani ikonta a komintin tsaro inda Jakadan kasar Taiwan ya rike kujerar kasar China har na tsawon shekaru 22, wato daga shekara ta 1949-1971 a lokacinda MDD ta amince da gwamnatin gurguzu ta kasar China.

=========================================================

Yau Lahadi 19-Mehr-1394H.SH=27-Zulhajji-1436H.K.=11-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 745 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Zulhajji-691H.K. Sheikh Muslihuddeen Sa’adi Shirazi babban malami marubucin wakoki ya rasu. An haifi Sa’adi a garin shiraz na kasar Iran, yay i karatunsa a gida da kuma makarantar Nizamiyya ta birnin Bagdaza na kasar Iraqi. Sa’adi yay i yawace yawace masu yawa a kasashen duniya ya kuma hadu da malamai da masana daban daban. Sa’adi shirazi ya rabuta littafai da dama fitattu daga cikinsu su ne Golistan, Bustan, da kuma Diwanin wakokinsa dukaninsu da harshen farisanci. Sa’adi yana daga cikin manya manyan malaman da suka bunkasa harshen farisanci a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 116 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Octoba-1899M. Aka fara yaki tsakanin Turawan Holanda mazauna kasar Afrika ta Kudu da kuma Turawan Ingila wadanda basu dade da fara mamayar kasar ba. Turawan Holanda ne suka fara zuwa Afrika ta kudu a cikin karni na 17 miladiyya, amma turawan ingila sun fara zuwa kasar ne a shekara ta 1841M. Bayan gano ma’adinai na zinari da luluu a kasar Turawan holanda sun so su kori turawan ingila daga kasar sai dai a karshen yakin turawan ingila sun sami nasara mallakar kasar, wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1931M a lokacinda turawan ingila suka mika mulki ga Fararen fata na kasar Holand.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Octoban-1991M. Aka wargaza hukumar yansandan ciki ta tarayyar Soviet wacce ake kira KGB a takaice. An kafa hukumar a shekara ta 1954M da nufin tabbatar da ikon jam’iyyar gurguzu ta tarayyar a cikin kasar sannan kula da harkokin tsaro na wajen kasar. KGB ta halaka masu adawa da tsarin komunisanci a cikin kasar da dama. Daga baya KGB ta zama hukuma mafi karfi a cikin tarayyar kasar wacce ta zama abin tsaro a cikin kasar da kuma wajenta. An wargaza hukumar KGB jim kadan kafin wargajewar tarayar a karshen shekara ta 1991M.

Yau Litinin 20-Mehr-1394H.SH=28-Zulhajji-1436H.K.=12-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa yau ce 20-Mehr ranar tunawa da Khoja shamsuddeen Mohammad Hafiz Shirazi. Babban malamin addini da kuma harshen farisanci. An haifi Hafiz Shirazi a shekara ta 727 H.SH a garin shiraz a nan Iran. Khoja Hafiz Shirazi ya haddace Al-qur’ani mai girma tun yana karami. Ya kuma taimaka so sai wajen bunkasa harshen farisanci a duniya da kuma al’adun Iraniyawa. Littafin diwan Hafiz wanda ya tattara wakokinsa ya sami karbuwa a cikin gida da kuma kasashen duniya har aka tarjama shi zuwa harsuna daban daban a duniya. Hafiz ya rasu a shekara ta 792 H.SH.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1373 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-zulhajji-63H.K. Aka aiwatar da kisan da ake kira waki’atu Harrah a garin Madina. Hakan ya auku ne shekaru biyu bayan shahadar Imam Husain (a) a karbala, inda Yazid dan Mu’awia ya aika muslimu bin Akaba tare da sojojinsa zuwa Madina inda suka kashe mutane , a fadin wasu malaman tarihu sun kai dubu 10. Daga cikinsu akwai sahabban manzon Al..(s) da dama. Kafin haka dai mutanen madina sun gaji da zaluncin Bani Umayya inda suka kora walinsu Marwan bin hakam daga Madina. Wani abin lura a nan shi ne Marwan bai fi shekaru 3 da rabi a kan gadon sarauta ba amma a cikinsa ne Ya kashe Imam Husain (a) a karbala, Ya kashe mutane Madina sannan ya sa aka kona dakin ka’aba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 147 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Zulhajji-1289H.K. Mulla Hakim Hadi Sabziwari babban malamin addini kuma masanin ilmin erfan ya rasu. An haifi Mulla Sabzivar a shekara 1212 H.K. Ya kuma shahara da sanin ilmin Fiqh, Tafsir, Abibin larabci, Mandiq, lissafi da magunguna. Mullah Sabzivar ya shahara har’ila yau da ilmin falsafa inda za’a gane matsayin a cikin ilmin cikin littafinsa mai suna «منظومه» . Har’ila yau yana da wasu litattafai wadanda suka hada da «اسرارالحکم» da kuma.. «الجبر و الاختیار»

=====================================================.

Yau Talata 21-Mehr-1394H.SH=29-Zulhajji-1436H.K.=13-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 69 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Octoba-1946M. Mutanen kasar faransa sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda aka rubuta bayan yakin duniya na biyu. Kafin haka dai an sha amun tashe tashen hankula na siyasa a kasar ta Faransa, wadanda suka santa shugaban rikon kwarya na lokacin Charles Digol ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar a cikin watan jenerun shekara ta 1946. Sannan aka rubuta sabon kundin tsarin mulki aka bukaci mutane sun kada kuri’ar jin ra’ayinsu kan sabon tsarin mulkin a ranar 13-Octoban-1946M. Digol ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar ya kafa jumhuriya ta 4 sannan ya kawo karshensa a shekara ta 1958M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 51 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Mehr-1343H.SH. Majalisar dokokin kasar Iran ta lokacin da kada kuri’ar amincewa da wata doka ta sanya rigar kariya ga Amurkawa mazauna na kasar Iran kan gurfana a gaban kotu a Iran bisa duk laifin da suka aikata. Wannan dokar wacce aka fi saninta da Kapitalasion-ta keta hurumin mutanen kasar Iran ta kuma wulakanta su. Da wannan dalilin ne Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayi wani jawabi mai zafi inda a ciki ya dira kan Sarki sha da kuma Amurkawa. Sanadiyyar wannan jawabin ne sarki ya tilasta masa gudun hijira a ranar 13- Aban-1343H.SH.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana 21-Mehr-1380H.SH. Aya. Abul Fadle Khunsari Najafi babban wakilin Imam Khomaoni (q) a yankin Araq ya rasu. An hafi Aya. Khunsari a shekarata 1295H.SH a Esfahan. Bayan kammala karatun sharar Fage a mahaifarsa ya je birnin Najaf na Iraqi inda fa kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin wadanda suka hada da Sayyeed Khuee, Sayyeed Hakim, da Aya. Garawi da kuma Mirza Zanjani. Bayan dawowarsa gida ya shiga cikin yunkurin ImamKhomni(q) na kawo gyara a kasar Iran, ya kuma taimaka musamman a shekarunda Imam yake gudun hijira. Bayan Nasra Imam Khomani (q) ya nadashi wakilinsa a yankin Araq a tsakiyan kasar Inya ya ci gaba da aiki har zuwa rasuwarsa.

==========================================================

Yau Laraba 22-Mehr-1394H.SH= 30-Zulhajji-1437H.K.=14-Octoba-2015M.

**Masu sauraro kun san cewa shekaru 201 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Octoba-1814M. Aka kafa majalisar Vienna a kasar Austria. Manufar kafa majalisar ita ce tabbatar da adalci da daidanto tsakanin kasashen Turai, musamma ganin yadda Sarki Napolio Banopora yake kokarin farwa wasu kasasheb yabki. Sai dai bayan da Napolio ya sake dawowa kan kujerar Mulki a karo na biyu a karshen watan Febrerun shekara ta 1815 na kwanaki 100 bayan da ya tsere daga inda ake tsare da shi, Majalisar Vienna ta tashi daga aiki. A cikin kwanaki 100 wanda Napolio ya yi a mulkinsa na biyu ya so ya sake mamayar wasu kasashen yankin, amma bayan an kasashen turan suka fi karfinsa a karo na biyu majalisar da dawo aikinta. Inda ta kamma aikin a cikin watan Yulin 1815M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 82 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Octoban-1933M. Kasar Jamus karkashin shugaban shugabancin Adolf Hitla ta fice daga kungiyar hadakan kasashen duniya wacce ake kira “Leaque of Nations”. Bayan yakin duniya na daya, an dorawa kasar Jamus takunkumai wadanda suka hada da takaita sojojinta. Amma bayan darewar Haitkan kan kujerar shugabancin Jamus ya samu sabani da sauran man ya manyan kasashen duniya wanda ya kai ga ya dukufa wajen kera makamai da kuma samar da rundunar sojoji mai karfi a kasar ta Jamus. Hakan ya gamu da rashin amincewar kasashen turai. Shi kuma don nuna fushinsa, shugaba Hitla ya fidda kasarsa daga kungiyar hadakan kasashen duniya ta :Leaque of Nations a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Octoban-199M. Julius Kambarage Nyerere tsohon shugaban kasar Kenya Tanzania ya rasu. An haife Nyerere a shekara 1922M. Bayan kammala karatu ya shi harkokin siyasa a shekara ta 1955M inda ya kafa jam’iyyar “Afrikan National Union Party”. A kasar Tangayika wanda yanki ne na kasar Tanzania a halin yanzu. A shekara ta 1961M Nyerere ya zama Priministen kasarsa, sannan a shekarar da ta biyo ya zama shugaban kasar Tangayika. Tare da kokarinsa ne kasashen Tangayika da Zanjibar suka dunkule suka zama kasar Tanzania a shekara ta 1964M. Nyerere ta ci gaba da zama shugaban kasar Tanzania har zuwa shekara 1955 inda ya sauka ya ci gaba da rayuwarsa har zuwa mutuwarsa a rana irin ta yau.

======================================================.

Yau Alhamis 23-Mehr-1394H.SH= 01-Muharram-1437H.K.=15-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau 01-Muharram-1437H.K. rana ta farko a kalandar hijira kamariyya, kalandar da musulmi suke amfani da shi wajen lisassafin ayyuka na ibada wadanda suka hada da azumi, hajji, watannin masu alfarma, shekarun balaga, da kuma makokin manya manyan magatan al-umma. A lokacin khalifinsa Khalifa na biyu aka fara amfani da wannan kalandar bayan ya shawarci Imam Aliyu dan Abitalib (a) wanda ya bashi shawarar ya fara daga hijirar manzon All..(s) daga Makka zuwa madina. Ana amfani da jujjuyawar wata ne wajen lissafin hijira kamariyya. Hakama hjira shamsiyya ana amfani da shekarar hijirar manzon Al…(s) ne daga Makka zuwa Madina, amma tare da amfani da lissafin jujjuyawan rana wato daga shekara 622 bayan haihuwar annabi Isa (a).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1440 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Muharram-07H.K. Manya manyan Kafiran Makka suka kulla wata yerjejeniya ta kauracewa musulmi da kuma dora masu takunkumin tattalin arziki bayan da suka bi duk hanyoyin sun kasa hana addinin Musulunci yaduwa. A lokacin ne Manzon All..(s) tare da danginsa da kuma sauran musulmi suka tari a wani kwari da ake kira sha’ab Abitalib. Wannan takunkumin ya ci gaba har zuwa shekaru ukku, wato zuwa watan Rajab shekara ta 10 da fara kira, a lokacinda wasu daga cikin shuwagabannin Kuraishawan suka ga yakamta a kawo karshen takunkumin bayan haka sai suka ga cewa gara ta cinya takardar yerjejeniya sai sunan Al..dake cikinsa. A karshen takunkumin ne manzon All..(s) ya rasa amminsa Abutalin(r) da kuma matarsa Khadiza (r).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Mehr-1361H.SH. Aya. Ata’ullah Ashrafi Esfani, wakilin Imam Khomani (q) a garin Kirmonsha kuma limamin masallacin jumma’a na garin yay i shahada.

Aya. Asharafi Esfani ya kasance jagora da mutanen Kirmonsh a lokacin gwagwarmaya da Tagoot, sannan bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci Imam Khomaini (q) ya nada shi a matsayin wakilinsa na garin Kirmonsha kuma limamin masallacin jumma’a na garin. Yana cikin wannan aikin ne munafukai makiya jumhuriyar Musulunci suka kashe shi a lokacinda yake bada sallar jumma’a a cikin Mehrabin masallacin.

========================================================.

Yau Jumma’a 24-Mehr-1394H.SH= 02-Muharram-1437H.K.=16-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Muharram.-61H.K. Ayarin Imam Husain (a) jikan manzon All..da iyalan gisansa sun isa kasar Karbala. Kafin haka watanni, dai Imam Husain (a) ya ki amincewa ya yi mubaya’a ga yazid dan mu’awiya a matsayin Khalifar musulmi. Sannan ya fita daga birnin Madina zuwa Makka inda ya zauna yan watanni. A lokacinne mutanen Kuffa suka bukaceshi ya je can wajensu ya jagorancesu. Dubbai daga cikinsu sun amince da jagorancinsa. Amma daga bayan don tsoron Abuidullahi bin Ziyad san saba alkawari. Sannan rundunar Hurr bin Ziyar mai dakoru dubu sun hana Imam Husain isa Kufa sun kuma tilasta masa zuwa karbala a rana irin ta yau. Wani abin lura a nan shi ne komandan sojojin Yazid Hur bin Ziyad ya tuba ya kuma koma bangaren Imam Husain (a) inda yay i shahada tare da su.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Octoba-1945M.aka kafa hukumar abinci da ayyukan noma ta duniya wacce ake kira FAO. Manufar kafa hukumar dai sun hada da bayarda taimakekkeniya tsakanin kasahen membobi a cikin kungiyar don wadatar da su da abinci, sannin sabbin dabarbarun noma, kasuwancin kayakin gona, da kifi. Hukumar FAO tana da majalisa wacce ta kunci mutane 34 wacce kuma take gudanar da taro bayan ko wani shekaru biyu. Hukumar FAO ita ce hukumar majalisar dinkin duniya mafi girma. Cibiyarta yana birnin Roma na kasar Italia. Har’ila kungiyar ta FAO ta maida ranar kafata a matsayin ranar abinci ta duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Mehr-1357H.SH. Aka yi kisan kiyashi na masallacin garin Kirmon a nan kasar Iran. Bayan kisan da sojojin sha suka yiwa mutanen Tehran a ci gaba da gwagwarmaya da suke yi da gwamnatin kasar, mutanen kirman sun taru a masallacin garin don yin addu’oeen cika kwanaki 40 da shahadar mutanen Tehran 18-Sharivar, amma sojojin sha suka fada masu suka kashe da dama daga cikinsu wasu kuma suka ji rauni. Hakan dai bai karawa sarkin kome ba sai bakin jina

=========================================================.

Yau Asabar 25-Mehr-1394H.SH= 03-Muharram-1437H.K.=17-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1430 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Muharram-08H.K. Manzon Al…(s) ya aike da wasiku ga sarakuna da shuwagabannin kasashen duniya yana kiransu zuwa Musulunci. Bayan kulla yerjejeniyar sulhu Hudabiyya da Quraishawa a Makka, manzon Al..(s) ya ga cewa dama ta samu na ya isar da kiran Musulunci ga manya manya da kananan kasashen duniya a lokacin. Malaman tarihi sun bayyana cewa wasikun da manzon All..(s) ya aika zuwa sarakunan da shuwagabannin kasashen dunia a lokacin sun kai 26. Ko wani shugaba da irin maida martani da yayi ga wasikar ta manzon All(s). A cikin sarakunan da suka ya aikawa wasikun dai sun hada da Roma, Farisa, Habasha, Bahrai, Yemen da sauransu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Muharram-61H.K. Umar bin Sa’ad ya isa kasar Karbala da rundunar sojojin Yazin wacce take da mayaka kimani 4000 don tilastawa Imam Husain (a) bai’a ga Yazid. Kafin haka dai Umar yana bukatar zama walin lardin Rai wanda Ubaidullah ya shardanta masa da cewa sai ya yaki Imam Husain zai amince masa da zama walin Rai. Kafin ranar 6 ga watan Muharram sojojin Umar bin sa’ad sun dara dubu 20. Ya yaki Imam Husain (a) sahabbansa a ranar 10-Muharram ya kashe su gaba daya, amma kuma abinda suka biyo baya sun hana shi burinsa na zama walin Rai.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 42 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Octoba-1973M. Kasashen larabawa wadanda suke da arzikin man fetur sun bada sanarwan sanya takunkumin sayar da mai ga kasashen Amurka da Britania da HKI sanadiyyar yakin da Larabawan suka shiga da HKI a ranar 6-Octoba na wancan shekara. Farashin man fetur ya daga so sai bayan wannan sanarwan. Takunkumin dai yay i tasiri sosai a kan wadan nan kasashe duk da cewa bai kawo karshen tallafin da wadan nan kasashe suke yiwa HKI kan larabawa ba. Har’ila yau wannan ya nuna cewa musulmi masu arzikin man fetur suna da makamai mai matukar muhimmanci don tallafawa lamuransu a duniya idan suna bukata.

. ======================================================

Yau Lahadi 26-Mehr-1394H.SH= 04-Muharram-1437H.K.=18-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Muharram-61H.K. Walin Kufa Ubaidullah bin Ziyad yay i wani jawabi a masallacin Kufa inda ya tara mutane ya fada masu cewa duk wanda ya ke goyon bayan Imam Husain (a) jikan manzon All..(s) zai kashe shi, kuma banda haka ya kira garesu da su shiga cikin rundunar da zata yaki Imam Husain (a) karbala.

Kadi sharia babban mufti na lokacin ya halatta jinin Imam Husain ya kuma yerjewa Ubaidullah bin Zaiyar ya yake shi. Daga nan ya bada unurni aka rufe kofofin shiga da fata na garin don hana wadanda zafi sabawa umurnin fata.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 148 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Octoba-1867M. Yankin Alaska ya zama wani bangare na kasar Amurka. Kafin haka dai kasar Rash ace take mallakar yankin. Amma sarkin Rasha na lokacin don tsananin bukatar kudi a lokacin ya sayar gwamnatin kasar Amurka yankin na Alaska mai arzikin man fetur da kuma rufe da dusan kankara. Rasha ta sai da Alaska ga kasar Amurka kan dalar Amurka miliyon $7.2 . Alaska yana da fadi kilomita murabba’I 1,500,000. Kuma tun shekara ta 1960 aka gano man fetur a yankin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 93 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Octoba-1927M. Aka bude radion BBC a kasar Britania. Da farko dai gidan radion mai zaman kansa ne, amma a shekara ta 1927 ya zama na gwamnatin kasar Britania. Sai kuma a shekara ta 1936 BBC ya fara watsa shirye shiryensa na Television. Ganin yadda kafar watsa labarai ta BBC ta sami karbuwa a kasashen duniya da dama gwamnatin kasar Britania ta yi amfani da kafar wajen yada manufofinta na mulkin mallaka da kuma manufofin sauran kasashen yamma na babakere kan siyasar duniya.

==========================================================

Yau Litinin 27-Mehr-1394H.SH= 05-Muharram-1437H.K.=19-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Muharram-61H.K. Ubaidullah bin Ziyad walin Kofa ya hada rundunar mayaka kimani 500 karkashin jagorancin Zuhair bin Kaisa, wadanda ba basu umurnin su tsare kofofin Kufa don kada wani ya fita ya je wajen Imam Husain (a). Amma duk da haka an sami wani jarumi mai suna Umair bin Abi-Salama wanda ya kutsa cikin sojojin Ubaidullah masu tsaron kofar fata daga kufa ya rinjayesu ya fice daga garin ya kuma je karbala inda ya hadu da imam Husain (a) ya kuma yi shahada a gabansa ranar 10-Muharram.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 39 da suka gabata a rana 19-Octoba-1976M. Hukumar leken asiri ta HKI Mosad ta kashe wani jigo a cikin kungiyar PLO ta Palasdinawa mai suna Ali Hassan Salama a birnin Berut na kasar Lebanon. Mosad ta makala wani bom a jikin motan Salama ta kuma tada shi. Wannan ba shi ne karon farko wanda HKI take kisan shuwagabannin Palasdinawa a cikin wata kasa ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Mehr-1366H.SH. Sojojin kasar Amurka a cikin tekun Farisa sun kai farmaki kan wani tsibiri mai rijiyoyin man fetur na Jamhuriyar Musulunci ta Iran mai suna Rustum a cikin tekun. Dalilin da gwamnatin kasar Amurka ta bayar na kai farmaki kan tsibirin Rustom na iran shi ne akwai na’urorin rada wadanda aka kafa a cikin tsibirin wanda ya kasance barazana tsaron kasar Amurka. Kafin haka kasar Kwait ta zargi Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cilla makaman linzami a cikin kasarsa. Amurka ta kai wannan harin ne a dai lokacinda kasashen Iran da Iraqi suka cikin yaki. Wannan kuma ya nuna yadda Amurka take nuna goyon bayan ga kasar Iraqi a yakin. Wanda ya nuna kariyarsu na cewa basa goyon bayan wani bangare a yakin.

=============================================================================.

Yau Talata 28-Mehr-1394H.SH= 06-Muharram-1437H.K.=20-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Muharram-61M. Habib bin Muzahir daya daga cikin sahabban Imam Husain (a) ya ne mi izininsa don kiran yan kabilarsa bani Asar wadanda basu yi nisa daga karbala don taimaka masa. Imam Husain (a) yay i masa izini ya kuma je wajensu ya kirasu zuwa taimakon Imam Husain (a) da kuma rabon duniya da lahira. Mutane 90 ne suka amsa kiran Habib bin Muzahir suka kuma kama hanya zuwa Karbala, amma sai suka gano cewa Umar bin Sa’ad yana da labari ya kuma aika mayaka 400 don hana su isa wajen Imam Husain(a). Hakan ya tilasta masu komawa gida. Da labarin ya isa kunnen Imam Husain (a) sai ya ce innalillahi wa ilaihi raji’un.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata wato 06-Muharram-61H.K. Imam Husain (a) a Karbala ya rubuta wata gajeruwar wasika mai wacce ta tattara ma’anoni masu yawa ga kaninsa Mohammad Alhanafiyya. Inda ya cike yake cewa –da sunan Al…mai rahama mai jinkai. Lallai duk wanda ya riskeni zai yi shahada wanda kuma ya bai yi haka b aba zai sami fatahi ba-Wannan wasikar tana da manufodi masu yawa, daga ci yana tabbatar da cewa Imam Husain (a) da sahabbansa sun san cewa dukkaninsu zasu yi shahada. Sannan duk wanda yake tare da shi, wanda kuma yake da wata manufa daban to kofa a bude take ya kama gabansa kafin lokaci ya kure masa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1031 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Muharram-406H.K. Sayyeed Muhammad bin Husain Musawi Bagdadi, wanda aka fi saninsa sayyeed radi. Ya rasu. Sayyeed Radi da yayansa Sayyeed murtada sun yi karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsu wadanda suka hada sheikh Al-mufid mafi sanin cikin malaman zamaninsu. Sannan sun zama manya manyan malamai tun suna matasa. Banda karantarwa Sayyeed Radi ya rubuta littafai fiye da 20 a fanonin ilmi daban daban. Mafi muhimmanci a cikin littafansa shi ne –Nahjul Balaga- inda sayyeed Radi ya tattara zababbun khudubobi, wasiku da gajejjerun kalaman Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Don muhimmancin wannan littafin a fagen ilmin addini da kuma balaga ta harshen larabci malamai da dama cikin shia da sunna sun yi masa sharhi. Sharifa Radi ya rasu yana dan shekara 47 a duniya.

=============================================================.

Yau Laraba 29-Mehr-1394H.SH= 07-Muharram-1437H.K.=21-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Muharram-61H.K. Komandan sojojin Yaziz a karbala Umar bin sa’ad ya bada umrnin a hana Imam Husain (a) da sahabbansa isa kogin Furat don shan ruwa.

Kafin haka dai walin Kufa Ubaidullah bin ziyad ya aike masa da wasi na ya hana Imam Husain (a) da sahabbansa shan ruwan Furat. Wannan halin ya ci gaba har zuwa daren 10 ga watan Muharram inda hadin yay i tsanani har zuwa lokacin shahadarsu bayan azahar.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 182 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Octobar-1833M. Aka haife Alfred Nobel masanin ilmin kimiyyar sinadarai dan kasar Sweden. Nobel yay i bincike mai yawa a bangaren ilmin kimiyyar sinadarai, har ya hada sinadarin Dainamaid wacce ake iya harhada boma bomai da shi. Nabel bai ji dadi ba ganin shuwagabannin duniya suna amfani da sinadarin ya gano wajen kisan mutane. Don haka a lokacin mutuwarsa ya bar wasiyya kan ayi amfani da dimbin arzikin da ya bari a rika bawa mutanen da suka yi fice a ayyukan ilmin da kuma samar da zaman lafiya a duniya wani bangare na kudaden da ya bari a ko wace shekara. Sai dai a halin yanzu shuwagabannin kasashen Turai sun shigarda harkokin siyasa a cikin kyautar ta Nobel, inda suke bada shi ga wadanda suke da hannu wajen kisan mutane.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Mehr-1357H.SH. Ma’aikatan ma’aikatar man fetur na kasar Iran sun fara wani yajin aiki wanda ya gurgunta aikin fitar da danyen man fetur na kasar zuwa kasashen waje da kuma na cikin gida. Yajin aikin ya zo ne a dai dai lokacin da juyin juya halin Musulunci karkashin jagorancin Imam Khomai (q) ya kusan kaiwa ga nasara. Ma’aikatan sun ci gaba da yajin aikin har zuwa nasarar juyin jua halin a ranar 22-Bahman-1357H.SH.

================================================================.

Yau Alhamis 30-Mehr-1394H.SH= 08-Muharram-1437H.K.=22-Octoba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Muharram-61H.K. Ruwan shay a kare a cikin hemomin Imam Husain (a) da iyalansa a Karbala. Khawarizmi ya kawo a cikin “مقتل الحسین” da kuma Khiyabani a cikin littafinsa “وقایع الایام” kan cewa a ranar 8-Muharram Imam Husain (a) da sahabbansa sun yi ta fama da karancin ruwa da kishi, sai Imam Husain (a) ya zagaya bayan Haima da kimanin kafa 19 sai ya tuna kasa, sai ga ruwa ya fara bubbuga, kowa ya sha aka kuma cika jakunkunan ruwa. Daga nan sai ruwan ya bace. Da labari ya kaiwa Abaidullah bin Ziyad labarin cewa an sami ruwa a hemomin Imam Husain (a) sai ya aikawa Umar bin sa’ad cewa ya gaggauwa gamawa da Imam Husain (a) ya kuma hana ruwa isa wajen. Daga nan Umar ya kara tsananta tsaro kan kogin furat. Wannan halin ya ci gaba har zuwa ranar 10-Muharram.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Muharram-61H.K. Imam Husain (a) ya aiki wani sahabinsa mai suna “Amr bin Qarzah”. Zuwa wajen Umar bin sa’ad shugaban sojojin yazid a karbala na su hadu a cikin dare tsakanin rundunoni guda biyu. Umar ya amsa gayyatar Imam Husain ya fito mutane 20 tare da shi sannan Umar ya fito tare da mutane 20 suka hadu a tsakiyar mayakansu. Da suka hadu sai Imam Husain (a) ya cewa mayakan da suka raka shi su koma in banda Abbas da dansa Aliyul Akbar. Sai Umar ba ya cewa mutanensa su koma , ya bar dansa Hafsin da kuma wani bawansa guda. Anan Imam Husain (a) ya tambayi Umar shin da gaskiya ne zaka yake ni? Sai Umar ya yi ta kawo uzurorinsa na cewa idan bai yake shi ba Ubaidullah zai rusa gidan, ko zai halaka danginsa ko zai kwace dukiyansa. Daga karshe Imam (a) ya dage kan yakarsa in bai yi bai’a ga yazid ba sai ya ce, masa, ..”na rantse da Al..baza ka dandani alkamar garin “Rai” wanda saboda kanason ka zaman walinsa ba. Sai ya juya ya koma wajen haimominsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 63 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Mehr-1331H.SH. Ministan harkokin wajen kasar Iran na gwamnatin Priminister Dr Mohammad Musaddiq ya bada sanarwan katse dangantakar Iran da gwamnatin kasar Britani. Husain Fatimi ya ce gwamnatin Dr Musaddi ta dau wannan matakin ne saboda dagewar kasar Britania wajen amincewa da hakkin mutanen kasar Iran na maida kamfanin man fetur wanda Britania ta mallaka a Iran ya zama na kasa. Sannan hakan ya faru ne bayan da majalisar ministocin kasar suka amince da hakan.

Add comment


Security code
Refresh