An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 17 January 2016 11:51

kasar kenya ta kara yawan dakarunta a kudancin kasar Somaliya

kasar kenya ta kara yawan dakarunta a kudancin kasar Somaliya
bayan harin da kungiyar Ashabab ta kai kan dakarun kungiyar AU, a kudancin Somaliya, kasar Kenya ta karfafa matakan tsaro a kan iyakan kasar da kudancin Somaliya. kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya nakalto wani babban jami'in tsaron kenya a jiya Assabar na cewa, Dakarun tsaron kasar sun karfafa matakan tsaro a kan iyakar kasar da Somaliya tare da kuma da kai hare-hare ta sama da ta kasa a kan sansanin mayakan Ashabab dake kudancin Somaliya.
a nasa bangare, kakakin tsaron kasar Kenya David Obonyo ya bayyana cewa kasar sa ta yi asara mai yawan gaske a kasar Somaliya, to amma hakan bai zai sanya ba su gajiya wajen irin taimakon da dakarun tsaron kasar sa ke bayar wa kalkashin Rundunar tsaro da Sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka wato Amisson , kuma kasar sa na da niyar kara yawan dakarun ta dake kasar Somaliya.

a ranar juma'ar da ta gabata ce, mayakan kungiyar Ashabab suka kai hari kan sansanin dakarun tsaro da sulhu na kungiyar tarayyar Afirka Amisson, inda suka hallaka sojoji 50, dukkanin su 'yan kasar Somaliya.

Add comment


Security code
Refresh