An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 January 2016 07:09

Iran:Saudiya Ba Za Ta Nasara Ba A Kan Nufinta Na Wargaza Yarjejjeniyar Da Ta Cimma Tare Da 5+1

Iran:Saudiya Ba Za Ta Nasara Ba A Kan Nufinta Na Wargaza Yarjejjeniyar Da Ta Cimma Tare Da 5+1
Ministan harakokin wajen Iran ya bayyana manufar kasar saudiya na  kawo cikas ga yarjejjeniyar da kasar ta cimma tare da manyan kasashen duniya tare kuma da kara rura wutar rikici a yankin gaba daya. Muhamad Jawad Zarif ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta iran ya bayyana cewa abin takaici wasu kasashen duniya sun yi ta kokarin sanya shamaki a yarjejjeniyar da Iran ta cimma tare da manyan kasashen duniya,bayan an cimma yarjejjeniyar wucin gadi a watan Nuwanban shekara ta 2013, magabatan birnin Riyad sun yi amfani da dukkanin karfinsu domin ganin wannan yarjejjeniya ba ta tabbata ba.ganin hakar su ba ta cimma ruwa ba, sai suke kokarin tayar da fitina tare kuma da rura wuta rikici a yankin baki daya.

 

Zarif ya ce ko shakka babu kisan mutane 47 a rana guda, daga cikinsu har da babban malamin ne shekh Namr Bakir Annamr wanda ya kwashe tsahon rayuwasa wajen fada da ta'addanci tare kuma da kare hakin Al'umma, ya kara fiddo manuufar magabatan saudiya a fili.

Har ila yau ministan harakokin wajen kasar ta Iran ya ce dabarun da  magabatan birnin Riyad suka yi na rusa yarjejjeniyar  ya gumshi ababe guda uku, na farko matsin lamba ga kasashen yamma na kadda su cimma wannan yarjejjeniya, sai kuma tsananta kai hare-hare wuce gona da iri kan Al'ummar kasar yemen da kuma yin abubuwan da za su tunzura magabatn birnin Tehran, dukkanin wadannan dubaru, ba za su ci narasa ba, batun harin da jiragen yakin saudiyar suka  kaiwa ofishin jakadancinmu dake birnin Sana'a na kasar Yemen kwa, mun tura rahoton a gabatan Majalisar Dinkin Duniya.

 

 

Add comment


Security code
Refresh