An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 January 2016 07:00

Yemen:Kungiyar Ansarullah Ta Gindaya Sharadi Na Tattaunawa Da Saudiya

Yemen:Kungiyar Ansarullah Ta Gindaya Sharadi Na Tattaunawa Da Saudiya
Kungiyar Ansarul…ta kasar yemen ta gindaya sharadin tattaunawa  da kasar Saudiya. A wata sanarta da ya fitar jiya, Muhamad Abdul-salam kakakin kungiyar Ansarul.. ya ce ba za su shiga tattaunawa ba da magabatan Riyad matukar ba a dakatar da harin wuce gona da irin da ake kaiwa kasar sa ba. Kakakin ya ce tattaunawar da aka yi cikin wata Decembar shekarar da ta gabata a birnin suizilland ta kumshi batutuwa guda biyu ne kawai, sakin firsinonin biyar da kuma kawo karshen killacewar da aka yiwa garin Ta'az. Har ila yau kakakin ya ce harin wuce gona da irin da saudiya ke kaiwa a kasar na gudana ne kalkashin jagorancin jakadan kasar Amurka dake birnin Sana'a

 

Yayin da yake ishara kan mayakan 'yan ta'addar IS da Alka'ida, Muhamad Abdul-salam ya ce wadannan kungiyoyi, magabatan watsinton da Riyad ne suka kirkiro su, idan kuma har da gaske suke suna yaki da wadannan kungiyoyi a duniya, to minene ya sanya ba sa kai masu hari a kasar ta yamen, yayin da suka kafa tutotinsu a manyan gine-ginen gwamnati da kuma bankuna a Makala babban birnin jihar Hadara maut.

 

 

Add comment


Security code
Refresh