An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 07 January 2016 10:44

Palasdinawa

Palasdinawa
Adadin Palasdinawan Da Su ka yi Shahada A cikin Shekarar 2015

An bayyana cewa a cikin shekarar 2015 da ta gabata adadin Palasdinawa da su ka yi shahada sun kai 79.

Kungiyar iyalan shahidan Palasdinawa ta fitar da wani bayani da a ciki ta bayyana cewa; A cikin shekarar da ta gabata ta 2015 adadin palasdinawa da su ka yi shahada sanadiyyar harbin sojojin 'yan sahayoniya sun kai 79, daga cikinsu da akwai kananan yara 35.

Kamfanin Dillancin Labarun (QUDSUNA) na Palasdinu ya ambato kungiyar ta iyalan palasdinawa wacce ta fitar da rahotonta na shekara-shekara a yau alhamis tana ci gaba da cewa; A tsakanin wadanda su ka yi shahadar da akwai mata 15 da kuma jariri guda dan watanni 3.

Wata kididdigar ta bayyana cewa daga lokacin barkewar boren Qudus a cikin watan Aprilu na 2015 zuwa yanzu, adadin palasdinawan da su ka yi shahada sun kai 147.

Add comment


Security code
Refresh