An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 30 December 2015 17:12

Wani Malamin Yahudawan Isra'ila Na Kira Zuwa Ga Kone Masallatai A Birnin Quds

Wani Malamin Yahudawan Isra'ila Na Kira Zuwa Ga Kone Masallatai A Birnin Quds
Wani daya daga cikin fitattun malaman yahudawan Isra'ila ya yi kira ga sauran yahudawa mabiyansa da su fara kona masallatai da majami'oin mabiya addinin kirista da suke cikin birnin Quds.

Shafin tashar talabijin ta Paletine Today ya bayar da rahoton cewa,a wata zantawa da malamin yahudawan mai suna Bent Scobchine ya yi da tashar talabijin mallakin gwamnatin yahudawan Isra'ila ta Channel 2 ya bayyana cewa, dole ne su kawo karshen duk wata alama ta wuraren bauta da ba na yahudawa ba a cikin birnin na Quds, da hakan ya hada da masallatan musulmi da kuma majami'oin kirista.

Bayahuden ya ce addinin kirista addinin ne na bautar gumaka, saboda haka ba shi wurin zama a cikin wannan birni.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wani malamin yahudawa ya yi irin wannan kira ga sauran yahudawan Isra'ila a kan musulmi da kiristoci dangane da kone wuraren ibadarsu ba.

Babban abin da yafi dagawa musamman mabiya addinin kirsiata mazauan birnin Quds hankali dai shi ne, yadda mutumin ya fito yana yin wannan kira kai tsaye a gidan talabijin na gwamnatin Isra'ila ba tare da wata fagaba ba, kamar yadda kuma babu wani mataki da aka dauka akansa a hukumance.

Add comment


Security code
Refresh