An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 December 2015 05:44

Jagora Ya Kai Ziyara Gidan Wasu Kiristoci Don Taya Su Murnar Kirsimeti

Jagora Ya Kai Ziyara Gidan Wasu Kiristoci Don Taya Su Murnar Kirsimeti
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kai ziyara gidajen iyalan wasu mabiya addinin Kirista da suka rasa iyalansu yayin kallafaffen yakin Iran da Iraki don taya su murnar bukukuwan Kirsimeti

Labarin da shafin Cibiyar Kula da kuma Wallafan Ayyukan Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya watsa ya bayyana cewar Jagoran ya kai wannan ziyarar ce a ranakun Kirsimetin don tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa (a.s) don taya mabiya addinin Kiristan murnar wannan rana.

Jagoran ya shaida wa daya mahaifiyar daya daga cikin sojoji Kiristocin da suka rasa rayukan na su a yayin kallafaffen yaki cewa kokarin sojoji ya samo asali ne daga irin kokarin mahaifansa mata.

A duk shekara dai Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Khamenei ya kan kai irin wannan ziyarar zuwa gidajen iyalan Kiristocin da suka rasa danginsu don jinjina musu da kuma taya su murnar bikin Kirsimetin.

 

Add comment


Security code
Refresh