An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 24 December 2015 11:13

An Yaba Da Kudurin Kwamitin Tsaron MDD Dangane Da Kasar Libiya

An Yaba Da Kudurin Kwamitin Tsaron MDD Dangane Da Kasar Libiya
Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Libiya Martin Kobler ya bayyana kudurin da kwamitin tsaron MDD ya fitar na goyon bayan yarjejeniyar siyasa da aka cimma a kasar Libiya a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske.

Kamfanin dillancin labaran Sharq al-Awsat na kasar Masar ya ce Manzon MDD na musamman din ya bayyana hakan ne a yau din nan Alhamis inda yace hakan wani kokari ne na tabbatar da tsaro da kuma cimma manufa ta siyasa da nufin ciyar da kasar Libiyan gaba

A jiya Laraba ce dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna goyon bayansa ga yarjejeniyar da bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar Libya suka cimma a makon jiya, na kafa gwamnatin hadin kan kasa. Kudurin kwamitin tsaron dai ya kuma kirayi kasashe mambobin Majalisar da kada su rika sayen mai daga hannun kungiyar ISIS da take rike da wasu yankuna masu arzikin mai na kasar Libiyan.

A halin yanzu dai, gwamnatoci biyu ne dai ake da su a kasar Libiyan wadanda ba shiri da junansu.

Add comment


Security code
Refresh