An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 18 December 2015 12:00

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi A Masar Ta Kira Zanga-Zanga A Duk Fadin Kasar

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi A Masar Ta Kira Zanga-Zanga A Duk Fadin Kasar
Kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kasar Masar zata gudanar da zanga-zangar tunawa da boren da ya kai ga kawo karshen mulkin kama karyar shugaba Husni Mubarak a shekara ta 2011.

 

A bayanin da kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kasar Masar ta fitar yana kira ga dukkanin magoya bayanta da sauran al’ummar kasar kan fitowa zanga-zangar gama gari a yau Juma’a domin tunawa da fara boren al’ummar Masar da ya kai ga kawo karshen mulkin kama karyar shugaba Husni Mubarak da ya shafe tsawo shekaru kimanin 30 a kan karagar mulkin kasar.

Bayanin ya kara da cewa ganin cikan shekaru hudu cur da kawo karshen mulkin kama karyar shugaba Husni Mubarak yana kara karatowa akwai bukatar fara gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar mai ci ta Abdul-Fatah Al-Sisi tare da jaddada bukatar sakin fursunonin siyasa ciki har da hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi.

A ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 2011 ne al’ummar Masar suka hada kai ta hanyar gudanar da taron gangami da zaman dirshen da nufin ganin bayan gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak, inda a ranar 11 ga watan Fabrairu na wannan shekarar matsin lamba ya tilasta masa yin murabus daga kan karagar shugabancin kasar.

Add comment


Security code
Refresh