An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 18 December 2015 11:56

Yan Sandan Turkiyya Sun Kai Samame Kan 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish

Yan Sandan Turkiyya Sun Kai Samame Kan 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish
Yan sandan Turkiyya sun kame wasu gungun mutane 11 a birnin Istambul karkashin shirin gwamnatin kasar na yaki da ta’addanci.

 

Kafar watsa labaran gwamnatin Turkiyya ta sanar da cewa; Jami’an ‘yan sandan kasar sun kai samame wani gida da ake zargin maboyar ‘yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish ne a garin Istambul cibiyar kasuwancin kasar inda suka yi nasarar kame mutane goma sha daya.

Majiyar tsaron kasar ta Turkiyya ta sanar da cewar bayanan sirri suna nuni da cewa ‘yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish suna shirya kaddamar da wani gagarumin hare-haren wuce gona da iri ne a birnin na Istambul. Kasashen Saudiyya da Qatar gami da Turkiyya dai sune ke goyon bayan ayyukan ta’addanci a Siriya da nufin cimma manufofinsu a kasar.

Add comment


Security code
Refresh