An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 18 December 2015 11:54

Sojojin Yahudawan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Musgunawa Palasdinawa

Sojojin Yahudawan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Musgunawa Palasdinawa
Sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan da Zirin Gaza.

 

Kafar watsa labaran Palasdinawa ta sanar da cewa; Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-haren ta’addanci kan Palasdinawa a yankin Zirin Gaza, inda suka jikkata Palasdinawa biyu ta hanyar harbi da bindiga tare da lalata gonakin noma.

A gabar yammacin kogin Jordan ma sojojin na haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi dauki ba dadi da ‘yan gwagwaryar Palasdinawa tare da jikkata Palasdinawa masu yawa tare da kame wasu adadi na daban.

Add comment


Security code
Refresh