An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 16 December 2015 05:51

Jam'iyyar ANC Ta Ki Amincewa Da Batun Sauke Shugaba Zuma Na Afirka Ta Kudu

Jam'iyyar ANC Ta Ki Amincewa Da Batun Sauke Shugaba Zuma Na Afirka Ta Kudu
Jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu ta sake jaddada rashin amincewarta da kiraye-kirayen da wasu suke yi na cewa shugaban kasar Jacob Zuma ya sauka daga karagar mulkin kasar biyo bayan matsalar tattalin arziki da kasar take fuskanta.

Kiraye-kirayen dai ya biyo bayan nada sabon ministan kudi na kasar ne wato David van Rooyen da masu adawar suke ganin ba shi da kwarewa a bangaren tattalin arziki suna masu cewa hakan wata alama ce da take nuni da tsaka mai wuyan da shugaban yake ciki wajen gudanar da bangaren tattalin arziki na kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a jiya ne dai jam'iyyar ANC mai mulki din ta sanar da rashin amincewarta da kiraye-kirayen da wasu suke yi na cewa wajibi ne shugaba Zuman ya sauka daga karagar mulkin kasar inda ta ce koda wasa ba za ta goyi bayan wannan yunkuri ba.

A baya ma dai masu adawar sun zargi shugaba Zuman da yin ta'annuti ga tattalin arzikin kasar zargin da ya ke ci gaba da musantawa.

Add comment


Security code
Refresh