An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 07 December 2015 13:55

Wani Masharhanci A Tanzaniya Ya Bayyana Bukatar Nahiyar Afrika Ga Sakon Jagora

Wani Masharhanci A Tanzaniya Ya Bayyana Bukatar Nahiyar Afrika Ga Sakon Jagora
Wani masharhanci kan harkokin kasashen musulmi a kasar Tanzaniya ya bayyana cewa; Sakon wasikar da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya aike ga matasan kasashen yammacin Turai ya fayyace hakikanin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

 

A zantawarsa da sashin Sawahilu na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a jiya Lahadi: Ibrahim Fili-Fili masharhanci kan harkokin kasashen Musulmi a kasar Tanzaniya ya bayyana cewa; Sakon Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya fayyace hakikanin makiya addinin Musulunci da kuma kokarin da makiya ke yi na bata sunan Musulunci ta hanyar danganta tashe-tashen hankula da kashe-kashenn gilla ga addinin.

Ibrahim Fili-Fili ya kara da cewa; Sakon wasikar ya kuma fayyace cewa; Musulunci addini ne na zaman lafiya da sulhu tare da watsa soyayya a tsakanin jinsin bil-Adama.

Har ila yau Ibrahim Fili-Fili ya fayyace cewa; kasashenmu na Afrika suna fama da wannan masifa ta ta’addanci, kuma a halin yanzu haka kungiyoyi da daman a ‘yan ta’adda suna gudanar da ayyukansu a nahiyar, don haka matasan nahiyar Afrika ma zasu iya amfana daga wannan sako na jagoran juyin juya halin na Musulunci a kasar Iran.

Add comment


Security code
Refresh