An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 07 December 2015 12:43

MDD Ta Yi Alawadai Kan Harin Da Aka Kai Wa Tchadi

MDD Ta Yi Alawadai Kan Harin Da Aka Kai Wa Tchadi
Majalisar dinkin duniya ta yi alawadai kan harin ta’addancin da aka kai a kasar Tchadi A wata sanarwa da ya fitar babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya bayyana cewa harin ta’addancin da ‘yan kungiyar boko haram suka kai tsibirnin Koulfoua  dake tabkin tsadi, shi ke kara nuna irin dabancin wannan kungiya, kuma sun yi alawadai da wannan ta’addanci.

 

Banki Moon ya meka ta’aziyarsa ga Gwamnati da Al’ummar kasar Tchadi musaman iyalan wadanda wannan hari ya ritsa da su.

A ranar Assabar da ta gabata ce wasu ‘yan gunar bakin wake uku da ake kautata zaton ‘yan boki haram ne suka tarwatsa bama-baman dake jikinsu a tsibirnin Koulfoua  dake tabkin tsadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30 da kuma jikkata wasu 80 na daban

Add comment


Security code
Refresh