An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 06 December 2015 15:08

Muhimmancin Wasikar Jagora Zuwa Ga Matasan Turai

Muhimmancin Wasikar Jagora Zuwa Ga Matasan Turai
Wani fitaccen marubuci dan kasar Italiya ya bayyana wasikar jagoran juyin juya halin muslunci zuwa ga matasan kasashen turai da cewa tan ada matukar muhimmanci.

Carlo Corbuci dan jarida kuma marubuci mai fafutukar kare hakkin bil adama a kasar Italiya ya bayyana a zantawarsa da gidan radiyon jamhuriyar muslunci ta Iran bangaren harshen Italiyanci cewa, hakika wannan wasika ta jagora tana tattare da fadakarwa ga matasan nahiyar turai.
Ya ce ko shakka babu wannan wasika ta jagora mutanen da suke da basira da kuma sanin inda aka nufa ne kawai za su iya fahimtar abin da ta kunsa yadda ya kamata.
Shi ma a nasa bangaren wani dan jarida fitacce a kasar ta Itakiya Sebastiano Caputo ya bayyana cewa, hakika wannan wasika za ta zama mai amfani ga matasan turai a yanzu da kuma a nan gaba.

Add comment


Security code
Refresh