An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 04 December 2015 06:33

Netanyahu Ya Yi Barazanar Rusa Masallacin Quds Mai Alfarma

Netanyahu Ya Yi Barazanar Rusa Masallacin Quds Mai Alfarma
Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi barazaar cewa zai iya rusa masallacin Quds cikin sauki ba tare da wani tayar da jijiyar wuya ba.

 

Netanyahu ya yi wannan barazana ne a daidai lokacin da hare-haren yahudawan sahyuniya kan masallacin Quds mai alfarma ke ci gaba da tsananta a cikin lokutan baya-bayan nan, inda yahudawa masu tsatsauran ra’ayi da ke samun kariya daga daruruwan ‘yan sandan Isra’la suke kai farmaki kan masallata a cikin masallacin tare da lakada msuu duka, da kuma harba musu barkonon tsohuwa.

A jiya jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun kame palastinawa 63 a yankin Kalkiliya da ke gabar yamma da kogin Jordan, daga farkon watan Oktoban da ya gabata ya zuwa yanzu palastinawa 109 ne suka yi shahada a hannun jami’an tsaron Isra’ila.

Add comment


Security code
Refresh