An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 01 December 2015 19:38

Taron Nuna Goyon Bayan Ga Al'ummar Palasdinu A Kasar Nigeriya

Taron Nuna Goyon Bayan Ga Al'ummar Palasdinu A Kasar Nigeriya
Ofishin jakadancin Palasdinu da ke tarayyar Nigeriya ya gudanar da bikin ranar nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu ta duniya.

 

Bikin da ya samu halattar wakilan kungiyoyi musamman masu zaman kansu na ciki da wajen Nigeriya gami da wakilan kabilu daban daban da kuma Palasdinawa mazauna kasar ta Nigeriya ya jaddada goyon bayansa ga al’ummar Palasdinu da ake zalunta.

Jakadan Palasdinu a Nigeriya Salih Fuhaid ya bayyana jin dadinsa kan wannan gagarumin taro da aka gudanar a Nigeriya domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu lamarin da ke fayyace cewa; Duniya tana nuna damuwarta kan siyasar zaluncin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke gudanarwa kan Palasdinawa.

Har ila yau mahalatta zaman taron sun yi suka kan yadda kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa suke daukan matakin siyasa mai fuska biyu kan matsalar Palasdinu tare da gudanar da mu’amala da haramtacciyar kasar Isra’ila tamkar halattacciyar kasa. Sannan suka jaddada wajabcin samar da yantacciyar kasar Palasdinu kuma Qudus ne babban birninta.

Add comment


Security code
Refresh