An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 30 November 2015 06:58

Sakon Jagora Karo Na Biyu Zuwa Ga Matasan Nahiyar Turai (2)

Sakon Jagora Karo Na Biyu Zuwa Ga Matasan Nahiyar Turai (2)
A jiya ne aka fitar da sakon jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei wanda ya aike zuwa ga matasan nahiyar turai.

 

A cikin sakon nasa jagoran juyin juya halin Musulunci ya ja hankalin matasan nahiyar turai da su zama cikin fadaka dangane da irin farfagandar da ake yadawa dangane da addinin muslunci a cikin kasashensu, musamamn ma yadda ake kokarin danganta addanin muslunci da ayyukan ta’addanci, alhali ta’addancin da ake gani sakamako ne na siyasar kasashen yammacin turai da kawayensu na yankin gabas ta tsakiya.

Jagoran ya yi ishara da irin matsanancin halin da aka jefa  ala’ummar palastinu tsawon shekaru fiye da 60 da suka gabata, inda yahudawan sahyuniya tare da goyon bayan Amurka da sauran kasashen turai suke yin kisan gilla a kan Palastinawa, wanda hakan babban ta’addanci ne da duniya ta kawar da kai a kansa.

Daga karshe ya kiraye matasan na turai da su bincike addinin muslunci da koyarwarsa, kuma su san addinin muslunci ta hanyar da ta dace, idan suka yi haka za su gane cewa addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da kare hakkin dan adam, sabanin abin da ake sanar da su.

Add comment


Security code
Refresh